Muna bai wa ’yan Najeriya haƙuri kan ƙaranci wutar lantarki — Ministan Makamashi




Ministan Makamashi, Bayo Adelabu, ya nemi afuwar ’yan Najeriya bisa rashin isasshiyar wutar lantarki da ake fuskanta a halin yanzu.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

A cewar Ministan, matsalar wutar da ake fama da ita a kwanakin nan tana da nasaba ne daga wasu ƙalubalai da suka dabaibaye fannin samar da lantarki.

Ya ce matsalolin sun fi ƙarfin ma’aikatar tasa a magance su cikin ƙanƙanin lokaci, wanda hakan ya haifar da ƙarancin wutar lantarki a ƙasar.

Sai dai ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za a fara ganin sauyi a fannin samar da lantarki a faɗin ƙasar.

A cewarsa, kafin ƙarshen shekarar nan, gwamnati na da burin cimma samar da isasshiyar wutar lantarki ga ’yan Najeriya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *