Wang Yi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Ministar Harkokin Wajen Birtaniya

[ad_1]

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da takwararsa ta Birtaniya Madam Yvette Cooper a jiya Alhamis bisa gayyata. Bangarorin biyu sun mayar da hankali kan musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Cooper ta bayyana ra’ayin Birtaniya kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, cewar bisa yanayin duniya na karuwar tashin hankali, Birtaniya na fatan kara tuntubar bangaren Sin don gaggauta kawo karshen yakin, da sake bude tattaunawa ta diflomasiyya, da neman mafita ta dogon lokaci.

Wang Yi ya bayyana cewa, ba wanda zai cimma nasara daga yaki marar karewa, kuma tsagaita wuta da dakatar da yaki shi ne burin jama’a. Bangaren Sin ya bukaci dukkan bangarori da su dakatar da ayyukan soja nan take, da warware sabanin ra’ayi ta hanyar tattaunawa bisa daidaito, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Ya ce, Sin da Birtaniya a matsayinsu na mambobin dindindin na kwamitin sulhun MDD, ya kamata su karfafa mu’ammala, su tsaya tsayin daka wajen aiwatar da matakai da suka dace da zaman lafiya, da kuma hada kai don kiyaye manufa, da ka’idodin kundin mulkin MDD, da ka’idojin kasa da kasa na wanzar da dangantaka, don hana sake tabarbarewar tsarin kasa da kasa da kuma lalacewar tushen zaman lafiya na duniya.

Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi kan dangantakar Sin da Birtaniya, kuma sun kai ga matsaya daya ta ci gaba da inganta dangantaka ta abota a dukkannin fannoni bisa manyan tsare-tsare masu dorewa tsakanin Sin da Birtaniya, ta yadda za a samarwa dukkanin fadin duniya kwanciyar hankali, da tabbaci duk da rikice-rikice da sauye-sauye da ake fuskanta. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *