An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Yanayin Bazara” A Brazil
[ad_1]
A ranar Laraba 18 ga watan nan ne, babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Brazil, suka gudanar da taron tattaunawa na duniya bisa taken “Sin a yanayin bazara: ci gaban Sin, dama ga duniya” a birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazil.
A yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, da ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Brazil Alexandre Padilha sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo. Kana, jakadan kasar Sin dake Brazil Zhu Qingqiao, da wakilai game da harkokin siyasa, da kasuwanci, da ilmi, da kafofin watsa labarai kimanin 120 sun halarci bikin.
Cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen duniya suna dogaro da juna wajen neman ci gaba da wadata. CMG za ta yi amfani da karfinsa na kasancewar kafar watsa labarai ta zamani, dake sahun gaba a duniya mai hade fifikon yada labarai da kirkire-kirkire na fasaha, da kuma albarkatun kafafen yada labarai, wajen inganta sakamakon tsarin zamanantar da al’ummar Sin, ta yadda hakan zai fi amfanar da duniya baki daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link