Za mu kawo ƙarshen yaƙin Iran nan ba da daɗewa ba — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce nan ba da daɗewa ba za su kawo ƙarshen hare-haren da suke kaiwa kan Iran, yana mai ƙoƙarin kwantar da hankalin kasuwannin duniya da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya girgiza.
Trump ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a jihar Florida, inda ya ce yaƙin zai kasance na ɗan lokaci kaɗan.
“(Yaƙin) zai ƙare nan ba da daɗewa ba, kuma idan ya sake faruwa, za su (Iran) fuskanci farmaki mafi tsanani,” in ji shi.
Maganar tasa ta taimaka wajen farfaɗo da kasuwannin hannayen jari, inda kasuwar Wall Street ta farfaɗo, yayin da kasuwannin Tokyo da Seoul ma suka buɗe da ƙarfi duk da ci gaba da tashin hankali a yankin.
A gefe guda kuma, farashin ɗanyen mai ya sauka da kusan kashi biyar cikin ɗari, bayan da ya haura dala 100 kan kowace ganga a ranar Litinin — mafi girma tun bayan yaƙin Rasha da Ukraine a 2022.
Sai dai rundunar juyin-juya hali ta Iran ta mayar da martani, tana cewa ita ce za ta yanke hukunci kan lokacin da za a kawo ƙarshen yaƙin, ba Amurka ba.
Sabon jagoran addinin, Iran Mojtaba Khamenei, ɗan tsohon jagoran Ayatollah Ali Khamenei, ya fara aikinsa da ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa kan Saudiyya, Bahrain, Qatar, Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa da kuma Isra’ila.
Haka kuma Iran ta ci gaba da rufe Mashigar Hormuz, wadda kusan kashi 20 na man fetur na duniya ke wucewa ta cikinta, lamarin da ya jefa kasuwannin duniya cikin fargaba.
A wani ɓangaren kuma, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa tare da abokan hulɗarta na shirin wani gudanar da wani aikin soji na haɗin gwiwa domin sake buɗe mashigar ruwan bayan rikicin ya lafa.
Yaƙin ya kuma ƙara tsananta a Lebanon, inda musayar wuta tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah ta kashe aƙalla mutum 486 tare da jikkata sama da 1,300 tun farkon watan Maris.