An sake gurfanar da waɗanda ake zargi da kashe uwa da ’ya’yanta 6 a Kano

[ad_1]



An sake gurfanar da maza huɗu a Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a unguwar Bompai, bisa zargin kashe wata matar aure, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi a farkon wannan shekara.

Waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Umar Auwalu, Yakubu Dayyabu, Isyaka Yakubu da Umar Ali.

Ana tuhumar su da laifukan kisa, fyade, fashi da makami da kuma kone-kone.

A lokacin shari’ar, uku daga cikinsu sun ce ba su aikata laifin ba.

Amma na farko, Umar Auwalu, ya amsa yawancin zarge-zargen da ake yi a kansa.

Duk da haka, saboda girman laifin, kotu ta rubuta cewa bai amsa laifin ba, kamar yadda doka ta tanada.

Lauyan gwamnati, Saleh Muhammad, ya tabbatar da cewa gwamnati a shirye take ta gabatar da hujjoji da kuma kawo shaidu don tabbatar da zargin.

Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotu, babban jami’i a ma’aikatar shari’a ta Kano, Salisu Muhammad Tahir, ya ce an raba shari’ar gida uku; K-54, K-55, da K-56.

Laifukan sun shafi kashe-kashen da suka faru a Tudun Yola, Dorayi Chiranchi, da kuma wani laifin fyaɗe da ake zargin sun aikata.

Ya bayyana cewa an samu amsoshi a cikin shari’o’i biyu, amma ba a iya ci gaba da ta uku ba saboda wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ba su da lauyoyi.

Ya ce ba za a iya ci gaba da shari’ar kisan ba tare da lauya ba, domin lamari ne na rai da mutuwa.

Tahir ya ƙara da cewa sun shigar da tuhume-tuhume da dama kuma suna shirye su gabatar da shaidu a zaman kotu na gaba.

Ya ce za su fara sauraron shari’ar a zaman kotu na gaba.

Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranakun 22, 27 da 28 ga watan Afrilu domin gabatar da shaidu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *