Adadin Lambar Shaidar Mallakar Kira Dake Hannun Kamfanoni Ya Kai Kaso 54% Na Jimillarsu A Sin

[ad_1]

Bisa rahoton binciken lambar shaidar mallakar kira ta kasar Sin na shekarar 2025 da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta fitar yau Laraba, karfin kirkirar kayayyaki masu lambar shaidar mallakar kira na Sin yana ci gaba da karuwa, inda kashi 87.4% na lambar shaidar mallakar kira na kamfanonin kasar aka bayar da su a bangaren nazari, wanda ya karu da kaso 0.8% idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Bugu da kari, adadin kayayyaki masu lambar shaidar mallakar kira da ke hannun kamfanonin Sin ya kai kaso 54.0% a shekarar 2025, wanda ya karu da kashi 0.7% idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Bugu da kari, rahoton ya kuma nuna cewa, tsarin kayayyaki masu lambar shaidar mallakar kira na Sin a kasashen waje yana bunkasa, inda kamfanonin da suka mika bukatarsu ta neman lambar shaidar mallakar kira ga kasashen waje suka kai kashi 24.7% a cikin kamfanonin da suka fitar da kayayyaki zuwa ketare, wanda ya karu da kashi 1.3% idan aka kwatanta da shekarar 2024.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *