Yadda Za A Magance Kaikayin Matse-matsi
[ad_1]
Daga Bilkisu Tijjani Kasim
Mafi yawanmu mun sani cewa kaikayin matse-matsi na daya daga cikin matsaloli dake addabar maza da mata tare da sanin cewa yana samuwa ne ta dalilin sanyi, wanda idan kaikayin ya zo koda cikin taro kake ko wani gurin jin kunya ba kowa ke iya daurewa wajen yin susa ba, sau da yawa akan sha maganin sanyi amma daga waje kaikayin bai fiya tafiya lokaci daya ta dadin rai ba.
Ga hanya mai sauki da zaku magance matsalar kaikayin matse-matsi in sha Allah.
Abubuwan bukata:
Jarkanwa da Mantafarnuwa
Sai kuma yadda ake hadawa:
Da farko za ku dauko Jarkanwa idan mai tauri ce za ku daka ta zamo gari, sannan Man Tafarnuwa, daga nan za ku samo karamar tukunya ku dora kan wuta ku zuba ruwa kofi daya, sannan ku dauki Jar Kanwa ku zuba cokali daya cikin wannan ruwan da kuka dora ku barshi ya tafasa sosai sannan ku sauke, bayan ya sha iska sai ku dauko Buta ku juye shi ku kawo Man Tafarnuwa ku zuba a ciki ku girgiza sosai.
Kafin fara amfani da wannan ruwan ku tabbata kun yi Shabing (aski) domin gurin ya zama babu gashi domin wasu lokutan barin gashin ma ya kan ta”azzara kaikayin, daga nan za ku dinga amfani da shi kullum kuna wanke gurin dake yi muku wannan kaikayin ko ciki ko waje. Da wannan za ku rabu da matsalar kaikayin matse-matsi in sha Allah.
[ad_2]
Source link