Tarihin Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku 1936-1959


Daga Idris Aliyu Daudawa

Na rubuta wannan labari nawa ne don in bayyana godiya ta ga Ubangiji, kuma mutane su san irin wahalhalun da ya sha kafin har ya kai ga samun mukamin Sarauta ta Sarkin Zazzau.

A cikin shekarar 1911, watau ina da shekara ashirin da hudu (24) da haihuwa ke nan, aka aika da ni zuwa makarantar Dan-Hausa da ke Kano. Na shekara daya a can na dawo gida.Ya ce ran nan ina zaune sai ga Shehu Baloha masinjan Joji, ya ce wai Joji ya na kira na a Bariki. Bayan da naje sai na ga Razdan ya dauki lambar Masinja ya lika mini a riga ta, ya ce ” Da ga yau ka zama Masinja” sai na durkusa na yi godiya. aka fada mini albashina sule Talatin (30).

Bayan na yi shekara uku ina wancan aikin sai rannan na roki Razdan ya maida ni makarantar Turawa ta Zariya, in rika koyawa ‘yan makaranta Larabci.

Razdan ya ce “A’a wannan aiki ba zai yi maka ba” saboda haka ya kai Magatakardar sa Malam. Kwasau can, Malami daya kuma Malam Umaru ya maida shi aikin Shanu, ni kuma aka hada mani aikin su duka, nake karbar Sule saba’in (70).

Ina cikin wannan aikin a cikin shekarar 1918 sai wani Hakimi na Zangon Katab ya taba kudin Jangali wato kashewa, aka raba shi da mukamin, ashe Allah ne ya nufa Sarautar a kaina ne zata fada, aka nada ni Hakimin Zangon Kataf na koma can.

Lokacin da na ke Hakimi a wancan Garin, na ga abubuwan Tashin hankali har biyu. wata shekara ina karbar Haraji sai Arnan Unguwar Gayya suka yi mani Tawaye. ina zuwa kauyen sai na ji sun dauki kuwwa, nan da nan sai suka taru makil, kowa daga kwari sai baka a hannun sa, sai ka yi tsammanin wani abu ne ya sa wannan boren. Dalili kuwa wai sun gaji da biyan Haraji ne kawai! Abu kamar wasa sai wani Arne wai shi Gankwan ya dana kibiya, yako duban ya sako mani ita. Amma sai ya kuskure ni ya samu Sarkin fada na a kafada. Yara na daga ganin haka sai suka yi kazam akan Arna! da Arnan nan suka ga bamu da wata alamar tsoro sai suka bada baya, suka shige Kurmi gidan Tsafi.

Mai martaba ne ya rubuta wannan labari na rayuwarsa da kansa mun samo shi ne daga kafar sadarwa ta Hadejia Ayau, wadda ita ma ta dogara ne da Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta 17 shekarar 1939.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *