Kwamitin Yaki Da Bala’u Na Sin Ya Kaddamar Da Ayyukan Kandagarki Da Rage Bala’un Lokacin Hunturu Da Bazara

[ad_1]

A yau Asabar, ma’aikatar kula da ayyukan gaggawa ta Sin, ta ce kwamitin yaki da bala’u na kasar ya sanar a kwanan nan cewa, akwai bukatar aiwatar da ayyukan kandagarki da rage bala’u dake aukuwa a lokutan hunturu da bazara, tare da la’akari da halaye, da yanayin bala’un yanayi, don tabbatar da tsaron rayukan jama’a, da dukiyoyinsu, da kuma kwanciyar hankali a fannin zamantakewa.

An kiyasta cewa, yawancin sassan Sin suna fuskantar babban hadarin yanayi mai sanyi, da kuma bala’un dusar kankara a lokacin hunturu da bazara. Hadarin gobarar daji a sassa da dama na kudancin kasar yana kaiwa babban mataki, kuma ana iya samun aukuwar bala’u da dama masu nasaba da ruwa a kusa da gabar teku.

Sanarwar ta bukaci a kara yin nazari, da tattaunawa kan halayen bala’u na lokacin hunturu da bazara, da bayar da gargadin bala’i kan lokaci, da aiwatar da tsarin “kiran gaggawa da samun amsa”, da tsarin gargadin gaggawa na aukuwar bala’u, da gudanar da binciken manyan kayayyakin more rayuwa, da wuraren ba da hidimomin jama’a, don tantance karfinsu na yaki da bala’u, da amfani da rawar da kwararrun masu fasaha ke takawa, da kuma karfafa wa jama’a gwiwa wajen bayar da gargadin aukuwar hadurra a yankunansu.

Bugu da kari, sanarwar ta jaddada cewa, ya kamata a gyara, da kuma inganta shirye-shiryen gaggawa game da bala’u masu alaka da ruwan sama, da yanayin sanyi, da dusar kankara, da kuma kankara a kan lokaci, tare da mu’amala da jami’an ceton gaggawa daban-daban a wuraren, da kuma adana isassun kayayyakin agaji na gaggawa. Bugu da kari, tana kira da a inganta karfin rigakafi, da kuma yaki da gobarar daji da ciyayi, da kuma kula da yadda ake amfani da wuta a sassa kamar na ayyukan noma da na gine-gine. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *