Yadda Muka Magance Rikicin Kabilanci Da Shaye-shayen Matasa A Masarautarmu —Sarkin Shukura

[ad_1]

Daga Rabiat Sidi Bala

Masarautar Shukra da ke kasar Ghana, daya ce daga cikin masarautun Hausawa masu dogon tarihi a kasar. A wannan tattaunawa ta musamman da Sarkin masarautar, wanda ya shafe shekaru 42 a kan karaga, ya bayyana abubuwa masu tarin yawa da tabbas masu karatu za ku so ku ji: Ga hirar kamar yadda wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta gudanar kamar haka:

Bari mu fara da takaitaccen tarihin mai martaba sarki

Da farko dai sunana Alhaji Ibrahim Hamidu Dantani. An haife ni a wurin da ake kira Sabon Zango cikin Accra a kasar Ghana. Daga nan ne fatauci na iyayena ya taho damu zuwa garin Shukura. A wannan lokacin Shukura dokar daji ne sosai babu lantarki, babu ruwa na fanfo sai rijiya. To, haka nayi rayuwa tare da iyayena biyu da kanina mai suna Haruna Tsoho, da wasu jama’a kadan a cikin Shukura. Haka rayuwa ta cigaba, lokacin da na girma na auri mata ta ta farko mai suna Hadiza Ibrahim, muka haifi ‘ya’ya tara, a cikinsu mata bakwai da maza biyu. Daga baya na auri mata ta biyu mai suna Zainab Raibero, ita ta fito cikin wata kabila da ake kira Ga, a cikin wannan kasar ba musulmai bane, amma Allah ya ba ni iko na mayar da ita musulma kuma na aure ta. Kuma a wurinta Allah ya ba mu baiwar ‘ya’ya maza biyu. Haka al’amarin ya tafi har lokacin da sarauta ya zo kaina a shekarar 10th August 1983. Bayan wasu shekaru kadan da nadin sarauta iyayena suka koma ga Allah, sai kuma shekaru biyu da suka wuce a lokacin nan kuma na rasa matata ta biyu. A yanzu shekara arba’in da biyu nake akan kujerar sarauta sai mu ce Alhamdulillah.

Zuwa yanzu sarakuna nawa aka yi a wannan masarauta ta Shukura?

A takaice dai sarakuna biyar aka yi a wannan masarauta ta Shukura. Na farko shi ne mai martaba sarki mai suna Atiya. Shekara uku ya yi a kan kujerar, sa’annan dan sa mai suna Haruna Atiya ya maye masa bayan rasuwar sa. Shekara biyu sarki Haruna yayi sarauta, ya koma ga Allah, sai mai martaba sarki Baba Mahmudu ya zauna a kan kujerar sarautar. Baba Mahmudu ya yi shekara daya shi ma ya koma ga Allah, sai sarauta ya koma ga hannun mai martaba Baba Zango. Bayan shekara uku Allah ya yi wa mai martaba Baba Zango rasuwa a lokacin ni ne Galadiman sa sai mutanen Shukura suka amince da cewa sarauta ta koma kaina. To yadda aka yi nake kan karagar mulki kenan har a yau.

Mai martaba sarki hakika mun samu labarin cewa, kusan ba a yi sarki da ya dade a kan karagar mulki kamar ka ba, shin mene ne sirrin dadewarka a sarauta?

To, farko dai sai mu ce Alhamdulillah, domin wani baiwa ne daga Allah ba iyawar mu ba ne. Ubangiji ne a cikin ikonsa ya ke aiwatar da abin da ya ga dama. Shi sirrin dadewa a kan karagar mulki daga Allah ne kawai.

Dole a cikin wannan tsahon tafiya da aka yi mai martaba sarki, akwai wasu abubuwa da aka fuskanta na kalubale, ko za ka iya bayyana mana babban kalubalen da ka fuskanta, wanda za a iya cewa kamar ta zamar maka wani rigakafi da ciyar da al’umma gaba?

To, a kwana a tashi a cikin tafiyar da lamari na sarauta dole za a sami wasu kalubale. Babban kalubale da zan iya cewa na fuskanta shi ne, a kan matasa maza da mata. Kan lamari na shan kwaya da sace-sace da rashin aiki na samari. To madalla, mun yaki wannan kalubale cikin iko Allah da taimakon gwamnati a lokacin da muka kai kara kuma ya saurare mu. Gwamnati ta yi mana goyon baya da ta taimaka mana muka hassasa wata kungiya da ke bibiyar masu kawo miyagun kwayoyi a cikin Shukura, ana kama su sa’annan kuma ana kama masu shan ta. Kuma ita gwamnatin ta gina mana babban ‘Police Station’ cikin Shukura inda ake jan kunnen masu wannan laifuka. Wannan ya sa muka sami saukin wannan kalubalen ya rage matukar ragewa, kusan ma nace mun rabu da wannan matsalar cikin ikon Allah.

Akwai wasu abubuwa da ke faruwa na rikice-rikicen kabilanci, musamman mu a Najeriya, kuma an samu hadin kan al’umma a karkashin masarautarka, maimartaba sarki ta ya ya ka iya cimma hadin kan kabilu daban-daban a masarautarka?

Ma sha Allah, haka ne rikice-rikicen kabilanci ya so ya ci mana gari wani lokaci a baya, amma da ikon Allah mun magance wannan rikice-rikicen. Da farko na yi kiran dukkan sarakan kabilar da ke cikin Zango Shukura da fadawa na kaf, muka tattauna game da samun sulhun wannan al’amari. Sai muka shirya wata kungiya da za mu sami kowane sakin kabila na Shukura ya na ciki kuma da ikon Allah mun kirkiro wannan kungiyar muka sa mata suna (Ablekuma Central Council of Zango Chiefs), amma a karkashin jagoran masarautar Shukura. Wannan kungiyar ta taimaka mana sosai ga samun hadin kan kabilu daban-daban sama da ashirin a Shukura.

Ko akwai wasu darusa da ka ke ganin ya kamata masarautunmu na Najeriya su duba su dauka, musamman wurin kan hadin kabilu, ga shi yanzu ana ta fama da rikice-rikice a wasu yankuna da yawa na kasa, kuma ya shafi rikice-rikice ne na cikin al’umma?

Darasi dai da zan iya bayarwa shi ne, kamar yadda muka magance wannan matsalar a kasar mu haka din idan za ku iya yi, to ina ganin za a sami sulhu a wannan rikice-rikicen na kabilanci.

A yankin masarautarka mai martaba, wane abu ne ka ke alfahari da shi?

Abin alfaharina na da yawa to, amma zan iya fadin daya, biyu zuwa uku. Na farko na hau kan kujera Shukura babu wuta na lantarki, amma a yanzu ko’ina akwai wutar lantarki duk fadin Shukura. Na biyu zama na a kan karagar mulki na Shukura mun sami ruwa na fanfo a kowane gida. Na uku mun sami hanyoyi na titi masu kyau wanda a da babu. Ga gidan likitoci daban-daban ‘Hospitals’, ‘Police Stations’, makarantu na islamiya da na boko da ma’aikata daban-daban.

Mene ne sakon mai martaba sarki ga al’ummar masarautar Shukura da makwaftansu, har ma da dukkan al’ummar Hausawa a duk inda suke a duniya?

Sako na shi ne ayi adalci, rikon amana da tausaya wa talakawa ga dukan dan’adam, balantana ma an dora maka jagorar al’umma a kan ka.

Ya ya mai martaba sarki yake ganin alakar gwamnatoci na siyasa da kuma masarautu a kasar Ghana?

Lalle alakar mu sarakuna da gwamnatocin siyasa a kasar mu Ghana na da tsari da aminci sosai. Saboda kodayaushe muka kai kukan mu suna sauraran mu a cikin lumana, girmamawa.

Ko akwai abin da mai martaba sarki ke son bayyanawa, wanda ba mu tambaye shi ba?

To abin da yayi saura shi ne, ina yi muku godiya ta musamman da wannan tambayoyin, domin daraja a gare ni da al’ummar Shukura bakidaya. Yadda kuka daraja mu Allah kuma ya daraja ku bakidaya, ya sanya haske a cikin aikin ku da daukaka. Alhaji Armiyawu Sulaiman Sarkin Dandawa na Shukura Ablekuma Central Allah ya kiyaye shi da iyalansa. Allah ya hada hankullan mu bakidaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *