Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu

[ad_1]



Fitaccen masanin karatu da ƙira’ar Al-Qur’ani kuma babban malamin nan da ke karantarwa a Masallacin Annabi da ke Madina, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba.

Shafin Al-Haramain ya ruwaito cewa Sheikh Bashir ya rasu ne bayan shafe kusan shekaru sittin yana koyar da Al-Qur’ani a Al-Masjid An-Nabawi da ke birnin Madinah.

Sheikh Bashir da aka haifa a shekarar 1358 Hijiriyya, wanda shi ne mafi shahara a cikin sahun bajiman malaman ƙira’a, ya rasu bayan shafe kusan shekaru 90 a doron ƙasa.

Fitattu daga cikin malamansa akwai Qari Fath Muhammad Panipati, da Sheikh Mahmoud Khalil Al-Husari, da kuma Sheikh Hussein Khattab, babban malamin ƙira’a na Sham.

Kazalika, Sheikh Bashir ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar Al-Qur’ani a ɗaya daga cikin masallatai mafiya daraja a duniya, inda ya koyar da dubban ɗalibai tsawon shekaru.

Wasu fitattu daga cikin ɗalibansa sun haɗa da: Sheikh Muhammad Ayyoub da Sheikh Ali Jaber – tsofaffin Limaman Harami guda biyu (Allah ya jikansu).

Akwai kuma Sheikh Muhammad Al-Mukhtar Al-Shanqiti — mamba a Majalisar Manyan Malamai ta Saudiyya da kuma Sheikh Abdul Muhsin Al-Qasim da Sheikh Salah Al-Budair — waɗanda a yanzu Limamai ne a Masallacin Annabi.

Marigayin yana daga cikin ginshikan da suka assasa tubali na ginin ilimin Qur’ani a Masallacin Annabi, inda ya bar tarihi mai albarka da kuma ɗalibai da dama da ke ci gaba da yaɗa ilimin Qur’ani a sassa daban-daban na duniyar Musulunci.

Allah Maɗaukakin Sarki ya jikan Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya karɓi ayyukansa na hidimar Al-Qur’ani, ya kuma ɗaga darajarsa a cikin sahun salihan bayi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *