Xi Da Takwaransa Na Aljeriya Sun Taya Juna Murna Kan Nasarar Harba Tauraron Dan Adam Na Aljeriya

[ad_1]

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Asabar ya yi musayar sakon taya murna da shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune kan nasarar harba tauraron dan Adam mai hangen nesa na Aljeriya daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin.

Xi ya ce aikin harba tauraron na dan Adam mai hangen nesa na Aljeriya, wanda ya biyo bayan harba tauraron dan Adam na sadarwa na kasar ta Aljeriya, wani hadin gwiwa ne da aka cimma nasara a kai tsakanin Sin da Aljeriya a fannin sararin samaniya, kuma wata muhimmiyar shaida ce ta cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Aljeriya.

A nasa bangaren, Tebboune ya ce nasarar harba tauraron dan Adam mai hangen nesa na Aljeriya wata babbar nasara ce a hadin gwiwar sha’anin sararin samaniya tsakanin Aljeriya da Sin, kuma wani sabon ci gaba ne a dangantakar kasashen biyu, wanda zai taimaka wa bangarorin biyu wajen fadada damarmakin kulla hadin gwiwa.

Kasar Sin ta harba tauraron dan Adam mai hangen nesa na kasar Aljeriya ne daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan da ke arewa maso yammacin Sin a yau Asabar.

An cilla wata rokar dakon kaya samfurin Long March-2C daga cibiyar ta harba tauraron dan Adam da karfe 12:01 na rana (agogon Beijing), inda ta yi nasarar aika tauraron zuwa da’irar sararin samaniyar da aka tsara.

Za a yi amfani da tauraron na dan Adam na Aljeriya ne musamman don tsara filaye da kuma rigakafin abkuwar bala’o’i da kuma rage radadinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *