Nijeriya Na Yunkurin Mayar Wa Da Manoman Tumatir Asarar Da Suka Yi Ta Naira Biliyan 1.3
[ad_1]
Gwamnatin tarayya ta yunkuro, wajen samar da shirye-shiyen magance asarar da mamoman Tumatir ke tabkawa a kasar.
Idan za a iya tunawa, a watan Mayun shekarar 2025 ne, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wataccen Abinci ta Tarayya, ta kiyasta cewa; cutar ta lalata gonakin da ake noman Tumatir, inda momansa suka yi asarar kimanin naira biliyan 1.3, wanda hakan ya kuma jawo tashin gwaron zabin Tumatirin a dukkanin kasuwannin kasar nan.
- Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
- Kawar Da Dukkanin Haraji Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar Sin Daga Afirka Zai Bunkasa Cinikayyar Albarkatun Gona Na Afirka Ta Kudu
Hakan ne ya sa, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wataccen Abinci ta Tarayya, ta kaddamar da wani shiri na musamman, don lalubo mafita a kan wannan matsala, domin dakile yaduwar cutar zuwa sauran gonakin da cutar ba ta kai ga yaduwa ba.
Misali, wata kwayar halitta da ke cin ganye da kuma sauran kayan lambu, na iya jawo wa manoma asarar da ta kai daga kashi 80 zuwa 100, matukar ba a dauki matakan kare ta da gaggawa ba.
Wanann na zuwa ne dai, bayan samun wasu rahotanni da aka alakanta su da barkewar annobar cutar a shakarar da ta gabata, da ake kira a turance, ‘Tuta absoluta’, wadda ta bulla a wasu gonakin da aka shuka Tutamar, musamman a jihohin Kano, Katsina da kuma Kaduna.
Bugu da kari, bisa wasu alkaluma da hukumar gudanar da bincike a fannin aikin noma ta kasa (NAERLS) ta fitar, sun bayyana cewa, a shekarar 2024 a kasar nan, an noma Tumatir, din da ya kai kimanin tan miliyan 3.73.
A cewar alkaluman, kimin hekta 824,000 manoman Tumatir a fadin kasar nan suka noma, wanda hakan ya nuna cewa; ba a iya samun wadataccen nomansa a shekarar ta 2024 ba.
Haka zalika, wannan fadakarwar za ta kara taimaka wa da kuma rabar da kayan aikin noman Tumatirin da suka kamata, musamman domin samar da daukin da ya kamata na dakile yaduwar wannana cuta da ke lalata gonakin da ake nomansu.
Kaza lika, a karkashin wani shirin noma na nau’ikan Tumatir da ake kira a turance ‘HORTITOM4’ da kuma ‘HORTITOM5’, wasu masu bincike ne a fannin nomansa suka kirkiro da su a shekarar 2025.
Mahukuntan, sun gudanar da yin gwaje-gwajen ne na wannan shiri a wasu gonakin, na yin noman na Tumatir da kuma a gonakin da ake yin nomansa da rani.
Wasu jami’ai a bangaren na noman nasa, sun bayyana cewa; wadannan nau’ikan na shirin noman Tumatirin, wato ‘HORTITOM4 da HORTITOM5’, sun kasance suna bijire wa dukkannin wani nau’i na cuta da za ta iya lalata shi, bayan an shuka Irin na Tumatirin.
Bugu da kari, manomi zai kuma iya samun yin girbin Tumatirin da zai kai daga kimanin tan 21.7 zuwa tan 27.2 daga cikin kowacce hekta daya da ya shuka Irin na Tumatirin.
“A kasar nan dai, Tumatir ba wai kadai ana nomansa tare kuma da yin amfani da shi ba ne, wata hanya ce da ke kara samar da kudaden shiga ga wadanda suka rungumi yin noman nasa, musamman a tsakanin kananan manoman da ke fadin wannan kasa.
Kasar nan dai, ta kasance tana daya daga cikin manyan kasashen da ke a nahiyar Afirka, wajen nomansa da kuma samar da shi mai dimbin yawan gaske.
Kazalika, a kwanakin baya, an ruwaito karamin Minista na Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wataccen Abinci ta Tarayya, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi ya bayyana cewa; fannin na kuma kara samar da ayyukanyi da yin jigilarsa zuwa kasuwanni, domin sayar da shi da kuma sarrafa shi zuwa wasu nau’ika daban-daban.
Bugu da kari, Hukumar Kula da Bincike Kan Harkokin Noma da Ayyukan Malaman Gona ta Kasa, wato NAERLS a cikin wani rahotan da ta fitar, ta sake bayyana sake bullar cutar ta Tuta absoluta a shekarar 2024, musamman a Jihar Kano.
[ad_2]
Source link