An Yi Musayar Kwarewa Game Da Ayyukan Rage Talauci Ga Masu Bukatar Musamman Na Sin a Dandalin FAO

[ad_1]

A yayin gasar wasannin Olympic ajin masu bukatar musamman ta lokacin hunturu ta Milan, an gudanar da wani taro mai taken “Raba hakkin ci gaba: Aikin rage talauci na masu bukata ta musamman na Sin” a hedkwatar hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO dake birnin Roma.

Yayin taron na jiya Alhamis, shugaban kungiyar masu bukatar musamman ta kasar Sin Cheng Kai, ya ce Sin ta sanya kawar da talauci ga masu bukatar musamman a matsayin muhimmin bangare na kawar da talauci, kuma masu bukata ta musamman miliyan 7 da dubu dari 1 a karkarar kasar Sin sun fita daga kangin talauci, inda Sin ta gano hanyar rage talauci, da hana komawa cikinsa saboda nakasa.

Babban daraktan hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO Qu Dongyu ya nuna cewa, kwarewar Sin ta zamo misali mai amfani ga al’ummar kasa da kasa, kuma FAO na son karfafa hadin gwiwa da bangaren na Sin.

Kimanin mutane 100 daga wakilan kasashe daban daban, da jami’ai da masana sun halarci taron, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan kwarewar rage talauci tsakanin masu bukata ta musamman na Sin, tare da tattauna hanyoyin ci gabansu. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *