Sinawa Masu Amfani Da Yanar Gizo Sun Kai Biliyan 1.125

[ad_1]

An fitar da “Rahoton binciken yanayin ci gaban yanar gizo na kasar Sin” karo na 57 a yau Alhamis 5 ga wannan wata, inda aka samar da alkaluma cewa, ya zuwa watan Disamban shekarar 2025, adadin masu amfani da yanar gizo a kasar Sin ya kai biliyan 1.125, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari na daukacin al’ummun kasar.

A lokacin da aka aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, tattalin arzikin dijital da fasahar AI sun samu matukar ci gaba a kasar Sin, musamman ma fasahar 5G da sauran manyan kayayyakin more rayuwar jama’a sun kai sahun gaba a duniya. Yanzu haka ana more fasahohin da abin ya shafa da sakamakon da aka samu da sauran kasashen duniya ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samar da dabarun kasar Sin ga ci gaban fasahohin zamani da dauwamammen ci gaba a fadin duniya. (Mai fassara: Jamila)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *