An kama wani mutum da ƙoƙon kan mutane 4 a Ogun
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Gafaru Rasaki bisa zarginsa da tono gawarwakin mutane daga maƙabarta da ke garin Sagamu tare da samun wasu kawuna guda huɗu.
Kakakin rundunar ’yan sandan, DSP Oluseyi Babaseyi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abeokuta, inda ya ce jami’an ‘yan sanda na shiyyar Shakura da ke Sagamu sun kama wanda ake zargin a ranar 21 ga watan Janairu, 2026.
“A ranar 21 ga Janairu, 2026, jami’an sashin ofisin ’yan sanda na Shakura sun kama wani Gafaru Rasaki da kawuna huɗu.
“Bayan an yi masa tambayoyi da cikakken bincike, an gano cewa wanda ake zargin ya tono gawarwakin mutanen ba bisa ƙa’ida ba daga maƙabarta.
“Wannan wani aiki ne da ya nuna rashin mutunta gawarwaki da kuma keta doka,” in ji Babaseyi
Babaseyi ya ce, an gabatar da abubuwan da ake zarginsa, inda ya ƙara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan aka kammala bincike.
Kakakin ‘yan sandan ya sake jaddada aniyar rundunar na kare lafiyar jama’a tare da gargaɗin cewa, duk wanda ke da hannu wajen tozarta gawar ɗan Adam zai fuskanci hukuncin doka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link