Mutane 18 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Jigawa — FRSC
[ad_1]
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane 18 a wani hatsarin mota da ya faru ranar Talata a Ƙaramar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.
Hatsarin ya faru ne a ƙauyen Danmasara da ke kan hanyar Dutse zuwa Kwanar Huguma, inda motocin Golf guda biyu da wata babbar mota suka yi karo.
- Sin Ta Gabatar Da Shirin Inganta Lafiyar Yara Da Matasa Na Nan Zuwa Shekarar 2030
- Jami’ar MDD: Kasar Sin Babbar Ginshiki Ce Ta Cinikayyar Duniya
FRSC ta ce gudun wuce ƙima, fashewar taya, da rashin ikon sarrafa mota ne suka haddasa hatsarin.
Mutane 20, ciki har da yara ne hatsarin ya rutsa da su.
Mutane 18 sun mutu nan take, yayin da direban babbar motar da mataimakinsa suka jikkata, an garzaya da su Asibitin Gabaɗaya na Dutse.
Jami’an agajin gaggawa na FRSC sun kwashe gawarwaki da waɗanda suka jikkata daga wajen tare da kai su asibiti.
Hukumar ta yi kira ga direbobi da su guji gudun wuce gona da iri, su kuma tabbatar da motocinsu suna cikin ƙoshin lafiya domin kauce wa asarar rayuka a gaba.
[ad_2]
Source link