Kwankwaso Ya Gargaɗi Masu Shirin Juya Masa Baya A Siyasar Kano


Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi gargaɗin cewa cin amana a siyasa ba ya samar da nasara mai ɗorewa.

Kwankwaso ya yi wannan jawabi yayin da yake magana da waɗanda suka amfana da shirin tallafin karatunsa.

  • Abiya Ya Zama Shugaban Jam’iyyar NNPP A Kano
  • APC Ta Shirya Karɓar Gwamna Yusuf — Abdullahi Abbas

Sai dai wasu na ganin Kwankwaso ya tura saƙon ne a matsayin gargaɗi ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu da ake zargin suna shirin koma wa APC.

Ya ce waɗanda suka bar tushen siyasa na iya samun nasara na ɗan lokaci, amma tarihi ya nuna cewa nasarorinsu ba masu ɗorewa ba ne.

Ya yi kira ga magoya bayan ‘Kwankwasiyya Movement’ da su kasance masu biyayya ga NNPP kuma su koyi darasi daga kuskuren da aka yi a baya.

Kwankwaso bai yi magana kai-tsaye kan kiran wasu mambobin NNPP ke masa ba na sauya sheƙa.

Shi ma Gwamna Yusuf bai yi bayani ba yayin da ake ta tsammanin yiwuwar sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *