Komawar Abba APC: Maslahar Al’umma Ko Kasuwar Bukata?

[ad_1]

Daga Abdullahi Muhammad Sheka

Batun yunkurin Sauya Shekar Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ce a halin yanzu ke daukar hankali, musamman yadda mabanbantan bayànai ke ta cinkaro da junansu, musamman Cewar da Ake shi Jagoran Darikar ta Kwankwasiyya da ake kallon a matsayin jangoran duk wata sabata juywra a farfakiyar Aiyasar Jam’iyyar NNPP na baya baya da wannan yunkurin.

Duk da cewa wasu masu hangen nesa na ganin wannan nokewar da Kwankwaso keyi bata wuce wani salon kawar da hankalin mkbiya ba, domin ko abaya haka ya Yiwa Jam’iyya PDP Lokacin da.kusiri aniyar dauko sabuwar Jam’iyya, inda ya.ruro su Abban cikin Sabuwar Jam’iyyar NNPP shi kuma da wasu tsiraru har sai da Suka zazzage Jam’iyyar PDPin wannan Suka jefar da ita.

  • Sin Ta Zurfafa Hadin Gwiwar Kasuwanci Da Abokan Huldar BRI A 2025
  • Habaka Layin Dogo Na Tanzaniya Da Zambiya Zai Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Wannan ce tasa ake kokonta bullar barakar da ake ta yayatawa tsakanin sa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, Wanda ya Kai a safiyar Litinin data Gabata Shugaban Jam’iyyar NNPP Hon Dugurawa ya Gudanar da Taron manema labarai inda ya mesanta kansu da Shirin Abba na komawa Jam’iyyar APC, Wanda har ya bayyana Wasu mutane Uku dabtkce sune ke Hada Gwamnan Abba da Kwankwaso, mutanen da Suka hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, Sunusi Suraja Kwankwaso da Sanata Rufa’i Sani Hanga.

Ana tsaka da tattaunawa Kan jawabin na Dugurawa ne kuma Gwamnatin Kano ta umarci Daukacin masu tike da musamman Gwamnati da shugabanni Jam’iyyar NNPP kowa ya koma Karamar hukumar sa domin fitar da matsayarsa Kan yunkurin na Gwamna don komawa Jam’iyyar APC.

Amma dai ana kyautata zaton wannan duk wani surkullen siyasa ne da aka tsara domin wata makiya mai tushe ta tseguntawa manema labarai Cewar tun an gama tsara yadda komawar Zata kasance da Kuma irin kwaakwarimar da za’a Yiwa tsarin inda da farko aka twkra

Murtala Sule Garo na iya zama mataimakin Abba idan shirin Gwamnan na komawa APC ya tabbata

Ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta kawo karshen alaarsa ta kusan shekaru arba’in da mai gidansa a siyasa Rabiu Musa Kwankwaso. Kasancewar shi kadai ne Gwamna a jam’iyyar NNPP, ficewarsa za ta sa a zahiri jam’iyyar ta bace daga jerin jam’iyyun da ke wata Dama Ci gaba dkbdamawk.

Wani hangen kuma shi ne Da yake jam’iyyar APC ta shirya gudanar da tarukan zaben shugabanninta a watan Fabrairu, Gwamna Abba na kokarin kammala shirinsa na shiga tarukan domin karbe cikakken iko da jam’iyyar a jihar Kano. Domin kara wa bangarensa karfin siyasa, majiyoyi sun shaida wa wannan manema labarai cewa Gwamnan ya dade yana shirya dabaru a boye domin samun goyon bayan ‘yan Majalisar tarayya, majalisar dokokin Jihar da shugabannin kananan hukumomi.

“Dan Majalisar Wakilai guda daya da aka tabbatar zai ci gaba da kasancewa tare da Kwankwaso shi ne surukinsa, wakilin mazabar Tarauni. Wakilan Nassarawa, Ungogo da Kumbotso kuwa suna shakku, suna auna yanayin siyasar,” Kamar yadda ake harsashe.

Aa gano cewa akalla ‘yan Majalisar dokokin Jihar NNPP 25 (biyu daga cikinsu sun rasu) daga cikin 27, ciki har da Kakakin Majalisar, Yusuf Falgore, sun amince da shirin Gwamnan na ficewa daga jam’iyyar ta NNPP. Sai dai majiyoyin sun Kara da cewa Gwamnan ya samu goyon bayan adadi mai yawa na shugabannin Kananan hukumomi.

Yayin da Wasu daga cikin shugabannin kananan hukumomin a halin yanzu suke biyayya ga Kwankwaso, amma dai ana kyautata zaton a karshe kusan dukkansu za su bi Gwamnan,” in ji majiyar.

Yayin da shirin ficewar Gwamnan ke kara karfi, Kwankwaso ya kira ‘yan Majalisar Dokokin Jihar zuwa wani taro a gidansa da ke Miller Road a ranar Juma’a data gabata, yayin taron, Sanata Kwankwaso ya shaida musu cewa a bayyane yake Gwamnan na shirin barin NNPP ya koma APC, don haka duk wanda ya zabi bin Gwamnan ya yi hakan.

Sai dai wata makiya ta tseguntawa manema labarai cewa Kwankwaso ya nuna takaicinsa, yana cewa ba a ba shi hujja mai gamsarwa kan dalilin da ya sa za su koma APC ba, yana mai jaddada cewa sun ci zabe ne da babu wani sai Allah. “Shin Allah da ya ba mu mulki a 2023 ba zai kasance tare da mu a 2027 ba?” in ji Kwankwaso, kamar yadda aka rawaito yana tambaya.

A karshen taron, ‘yan majalisar sun amince su gana da Gwamnan domin a ba da dama ta karshe ga tattaunawar, ta yadda duk watw shawarar siyasa da Gwamnan zai dauka, a dauke ta tare da Kwankwaso.

Sai dai wata majiya ta shaida cewa lokacin da ‘yan majalisar suka nemi ganawa da Gwamnan bayan taron na Miller Road, Gwamnan ya ce ya riga ya ji duk abin da ya faru a taron, kuma shawarar da ya yanke na shiga APC ba za a iya sauya ta ba.

Sai dai Kuma idan ba’a yi sa’a ba, wannan guguwar Sauya Shekar na Shirin yin awon gaba da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam domin akwai Yiwuwar tsige mataimakin gwamna. Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, na iya zama mutum na farko da zai fada cikin guguwar siyasar da ke shirin afkawa jam’iyyar NNPP a Kano.

A wani bangare na shirin Gwamnan na samun goyon bayan manyan jiga-jigan APC a Kano, ana shirin miaa sunan tsohon dan takarar mataimakin gwamna na APC a zaben 2023, Murtala Sule-Garo, domin maye gurbin Abdulsalam. Haka kuma, ana shirin mika sunan tsohon dan takarar Gwamna na APC a 2023, Nasiru Gawuna, a matsayin dan takarar Sanata na Kano ta tsakiya a 2027.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *