Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

[ad_1]


Tsohon Mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya, ya tabbata bai da masaniya kan ƙalubalen tsaron da Nijeriya ke ciki.

A ‘yan kwanankin da suka gabata ne dai, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sada zumunta, yana ikirarin cewa, ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya, inda ya ce, ya saka Nijeriya a jadawalin kasashe masu damuwa ta musamman, kuma ya yi barazanar daukar matakin soji kan “‘yan ta’adda da ke kai wa Kiristoci hari.”

Da yake mayar da martani kan wannan batu a wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE, a ranar Talata, Sanata Ndume ya ce kalaman Trump sun nuna rashin fahimtar kalubalen rashin tsaro da Nijeriya ke fuskanta.

Ya ce, “Wannan ba yana nufin ba a kashe Kiristoci ba ne.” Abin da muke faɗa shi ne, ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba – ana kashe Musulmai ma,”

“Addinan biyu sun tabbatar da hakan, akwai kashe-kashen rayuka da yawa da ke faruwa a Nijeriya tsawon shekaru 16 da suka gabata da kuma fiye da haka daga rikicin Boko Haram a 2009. Babu wanda zai iya musanta hakan.

“Amma a ce kawai ana kai wa Kiristoci hari ya dogara ne da inda abin ya faru. Idan ya faru a yankin da Kiristoci suka mamaye, a zahiri Kiristoci ne za su kasance waɗanda abin ya shafa kamar yadda yake a yanzu a Benuwe da Filato.

“Idan ya faru a yankin da Musulmai suka mamaye, ya danganta da irin abin da ke faruwa a can, waɗanda abin zai shafa a zahiri Musulmai ne.

“Idan aka kai hari a coci, waɗanda abin zai shafa za su zama Kiristoci, haka idan a masallaci ne, Musulmai ne za su kasance waɗanda abin ya shafa. Wannan shine gaskiyar magana,” in ji Sanata Ndume.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *