Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka
[ad_1]
Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa NPA ta Kasa Dakta Abubakar Dantsoho, ya bukaci kasashen da ke a Afrika ta Yamma da na Afirka ta Tsakiya da ke cikin kungiyar da ke Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Afirka wato PMAWCA, da su kara karfafa hadaka, domin cin gajiyar albarkatun da ke a fannin.
Ya yi wannan kiran ne, a ranar Laraba a taron kungiyar karo na 45 na shekara-shekara da ya gudana a birnin Pointe-Noire, na Jamhuriyar Kongo.
Dantsoho ya ci gaba da cewa, hakan zai kuma taimaka wajen kara habaka kasuwanci a Afirka da kuma bunkasa tattalin arzikin da ake samu na Teku.
A cikin sanarwar da Shugaban wanda kuma shi ne, Shugaban kungiyar ta PMAWCA, ya kara da cewa, kasashen da ke a cikin gungiyar na da kamanceciya wajen bunkasa fannin.
Dantsoho wanda Ikechukwu Onyemekara, Janar Manaja a bangaren hudda da jama’a a Hukumar ta NPA ya wakilce shi a wajen taron ya ci gaba da cewa, kungiyar na kara mayar da hankali a fannin sauyin yanayi da samar da makamashi, wanda wadannan abubuwan su ne, ginshiki ga ayyuakn na Tashoshin Jiragen Ruwa.
Shugaban ya bayyana cewa, taron ya kuma mayar da hankali wajen wanzar da tsare-tsare, inda hakan ne, itama Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali a kai.
“Tekunan da suke a tsakanin kasasehn sun kasance wani babban nauyi a kan mu na tabbatar da cewa, kasashen da ke a cikin kungiyar, sun amfana da su,” A cewar Shugaban.
Shugaban ya kuma bukaci mahalarta taron da su dauki kansu a matsayin jakadun bunkasa makomar fannin tattalin arzikin Afrika.
Ya kara da cewa, kara ingnata kayan aiki da ke a Tashoshin Jiragen Ruwa da kara bunkasa tsaro da tabbatar da ana bin ka’ida.
Shugaban ya kuma yabawa Gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Kngo da kuma alummar kasar, bisa karbar bakuncin taron kungiyar a sakatariyar ta da ke a kasar
[ad_2]
Source link