Abubuwan Da Ke Haddasa Gobara A Lokacin Sanyi Da Hanyoyin Kare Su


Yayin da yanayin sanyi ko hunturu ke ƙara shigowa a wasu sassan Nijeriya, za a lura da iska mai sanyi, hazo da kuma ƙura na yawaita. Sai dai kuma a wannan yanayi ana fuskantar yawaitar gobara.

Daga watan Disamba zuwa Maris, hukumomin bayar da agajin gaggawa da ma’aikatan kashe gobara sun sha yin gargaɗi kan yawaitar aukuwar gobara a gidaje da kasuwanni da ma’aikatu, lamarin da ke barazana ga rayuka, dukiyoyin jama’a.

  • Yadda Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan ‘Yan Jarida 7 A Gombe
  • NSCDC Ta Kama Mutane 3 Kan Kisan Jami’inta A Kano

Yanayin Sanyin Da Ke Haddasa Gobara

Lokacin sanyi na zuwa da busasshiyar iska da bushewar ciyayi da shuke-shuke. Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA), ta bayyana cewa irin wannan yanayi na sa kayayyakin amfani a gida da ciyayi su zama masu saurin kamawa da wuta. Da zarar wuta ta tashi, iska kan taimaka wajen yaɗa ta cikin sauƙi.

Jami’an aikin kashe gobara sun bayyana cewa komai ƙanƙantar wuta tana iya haddasa gobara, misali wutar kyandir, wutar girki, wutar maganin sauro na iya rikiɗewa zuwa gobara a lokacin sanyi, saboda sauƙin kamawa da kuma yadda iska ke taimaka mata ta bazu.

Manyan Abubuwan Da Ke Haddasa Gobara A Lokacin Sanyi

Hukumomi a matakai daban-daban sun bayyana cewa abubuwan da ke haddasa gobara a wannan lokaci sun haɗa da sakaci da kuma yanayin muhalli.

1. Sakaci Da Wuta A Gida

Wasu mutane kan yi amfani da kyandir, fitilar ƙwau ko wutar garwashi da nufin ɗumama ɗaki ba tare da mayar da hankali ba. Idan aka bar wutar tana ci ba tare da kulawa ba, musamman idan mutane suka yi barci da ita a kunne, hakan na iya haddasa gobara.

2. Barin Girki A Wuta Ba Tare da Kulawa Ba

Hukumar kashe gobara ta tarayya da na jihohi sun bayyana cewa barin abinci a kan wuta ba tare da kula da shi na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa gobara a gidaje, musamman a lokacin bukukuwa inda ake yin girke-girke masu yawa.

3. Matsalar Wutar Lantarki

A birane, mafi yawan gobara na aukuwa ne sakamakon lalacewar wayoyin lantarki, lalacewar mahaɗar wayoyi, ko kuma kamawar wuta bayan hukumomi sun dawo da lantarki. Rashin duba kayan lantarki akai-akai na iya haddasa gobara cikin sauƙi.

4. Ƙona Daji Da Shara

A yankunan karkara da ma birane, mutane kan ƙona shara ko gonaki. Amma a lokacin sanyi, irin wannan wuta ta kan kama sosai saboda bushewar ciyayi, wanda hakan yana haddasa gobara a gidaje da gonaki.

5. Ajiye Abubuwan Da Ke Saurin Kamawa da Wuta Ba Daidai Ba

Ajiye fetir, gas, ko wasu abubuwa masu saurin fashewa ko kamawa da wuta a cikin gida ko kusa da wuta na ƙara hatsarin tashin gobara. Hukumomi sun sha gargaɗin jama’a kan ajiye fetir a gidaje.

Tasirin Gobara Ga Al’umma

Gobara a lokacin sanyi na lalata gidaje, shaguna da kasuwanni, tana tilasta wa mutane barin muhallansu, tare da jawo asarar dukiya da hanyoyin neman rufin asiri. Hukumomi sun jaddada cewa rigakafi ya fi magani, musamman ganin cewa kayan aikin kashe gobara ba su wadata a wasu yankuna ba.

Hanyoyin Kare Kai Daga Gobara

Ga wasu hanyoyi da hukumomi da suka zayyano da za su taimaka wajen hana aukuwar gobara:

1. Kashe Kayan Lantarki

Ake tabbatar da cewa an kashe ko kuma an cire kayan wuta daga lantarki idan ba a amfani da su, musamman kafin kwanciya barci ko kuma lokacin fita daga gida.

2. Kula Da Duk Wani Abu Da Aka Ɗora A Kan Wuta

Kada a bar girki ko wutar kyandir ba tare da kulawa ba. A tabbatar an kashe wuta kafin a kwanta barci. A nesanta yara daga ɗaukar ashana da amfani da duk wani abu da zai iya haddasa tashin gobara ko wuta.

3. Guje Wa Ƙona Daji Ko Shara

Hukumomi da na agajin gaggawa sun haramta ƙona shara da daji a lokacin sanyi, saboda hatsarin yaɗuwar wuta.

4. Ajiye Abubuwa Masu Saurin Kamawa da Wuta

Gujewa ajiye gas a wajen zama ko cikin ɗaki. Ka da a ajiye fetir ko sinadarai masu saurin tashi ko kamawa da wuta a cikin gida ko kusa da wuta.

5. Samun Kayan Kashe Gobara A Gida

Ajiye abun kashe gobara, botiki ɗauke da yashi, ko ruwa na iya taimakawa wajen dakatar da ƙaramar gobara kafin ta bazu.

6. Sanin Lambobin Agajin Gaggawa

Hukumomin NSCDC, NEMA da Ma’aikatar Kashe Gobara sun buƙaci jama’a suke adana lambobin agajin gaggawa domin neman ɗauki a kan lokaci.

Yanayin sanyi ya kasance lokaci na taka-tsan-tsan a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya, saboda bushewar ciyayi da bishiyoyi da iska mai ƙarfi. Duk da haka, ana iya kaucewa aukuwar gobara idan mutane sun bi ƙa’idojin tsaro da shawarwarin hukumomi, ta hanyar kulawa da wayar da kai, al’umma za su iya kare rayukansu da dukiyoyinsu.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *