Sashen Sayayya Da Kashe Kudade Na Kasar Sin Na Samun Bunkasa Ba Tare Da Tangarda Ba A Hutun Bikin Bazara

[ad_1]

Sinawa masu sayayya da kashe kudaden biyan bukatu sun shiga hutun bikin bazara tare da karin kashe kudi mai yawa, inda suke cika gidajen cin abinci da manyan kantuna, da tafiye-tafiye a fadin kasar, wanda hakan ya ba da damar samun bunkasar bangaren sayayya da biyan bukatu a farkon shekara.

A cewar bayanan da suka fito daga ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, a cikin kwanaki hudu na farkon hutun, matsakaicin cinikin da ake yi kullum a manyan shagunan dillalai da na abinci ya karu da kashi 8.6 daga na makamancin lokacin a bara. Yawan zirga-zirga da kuma kudaden shiga a manyan titunan kasuwanci da yankuna 78 a cikin kwanaki ukun farko, ya karu da kashi 4.5 da kuma kashi 4.8, bi-da-bi.

A ranar 17 ga watan Fabrairun bana ne aka yi bikin bazara, wanda kuma ake kira da sabuwar shekarar gargargajiya ta Sinawa, kana hutun da ake yi wanda aka fara kwanaki biyu kafin ranar, zai gudana har na tsawon kwanaki tara.

Kudaden da ake kashewa a bangaren bayar da hidimomi su ma sun karu sosai. Mizanin kudin da ake kashewa wurin yawon bude ido na cikin gida da ke kan manyan dandaloli ya karu da kashi 4.5 a ma’unin shekara-shekara a cikin kwanaki uku na farkon hutun, gami da karuwar kashi 26 cikin dari a bangaren hayar motocin hawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *