Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS

[ad_1]



Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.

Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.

Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.

A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.

A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *