Shugabannin Kasashe Da Na Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Taya Murnar Bikin Bazara Na Sin

[ad_1]

Kwanan nan, shugabannin wasu kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa da dama sun buga waya ko aikewa da sakwanni ga babban sakatare na kwamitin koli na jam’iyyar JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, don taya jama’ar kasar murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya.

Shugaban kasar Comoros Azali Assoumani ya bayyana fatansa na ganin kasar Sin ta kara taka rawarta a dandamalin kasa da kasa, da kara samun sabbin nasarori wajen neman muradun bai-daya na al’ummar Sin da duk bil’adama, da kuma inganta zaman lafiya da ci gaban duk duniya.

A nasa bangare, shugaban kasar Gabon Brice Clotaire Oligui Nguema ya bayyana cewa, Bikin Bazara biki ne mai dogon tarihi, wanda ke kunshe da ma’anar zaman lafiya da fatan alheri. Gabon na fatan karfafa dangantakar sada zumunci da hadin gwiwa tare da kasar Sin, domin samun ci gaba da wadata tare.

Baya ga haka kuma, shugabannin kasashen Seychelles, Botswana, Somalia, Afirka ta Tsakiya, Mongolia, Armenia, Iran, Isra’ila, Tunisiya da Ostiriya su ma sun buga waya ko aikewa da sakwanni ga shugaba Xi Jinping don taya murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin, tare da yi wa jama’ar kasar fatan alheri, da kuma yi wa kasar fatan kara samun ci gaba da wadata. (Mai fassara Bilkisu Xin)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *