Ramadan: Hisbah Ta Kama Mutane 9 Bisa Zargin Cin Abinci A Bainar Jama’a


Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu Musulmai tara bisa zargin cin abinci a bainar jama’a a ranar Laraba, ranar farko a watan Ramadan.

Mataimakin Kwamandan Hisbah, Mujahid Aminudeen, ya ce wadanda ake zargin sun hada da mata biyu da maza bakwai.

Ya bayyana cewa, an kama su ne bayan an gan su suna cin abinci da rana tsaka, saɓanin dokokin azumi.

“Mun kama su kuma suna tare da mu, za mu sanar da su muhimmancin azumi, yadda ake yin Ibada da karatun Alƙur’ani, da kuma yadda za su zama Musulmai nagari,” in ji Aminudeen.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *