Sin Za Ta Aiwatar Da Manufar Harkokin Kudi Mai Inganci A 2026
[ad_1]
An gudanar da taron ayyukan kudi na kasa na Sin a birnin Beijing, a jiya Asabar zuwa yau Lahadi. Taron ya nuna cewa, kasar Sin za ta aiwatar da manufar harkokin kudi mai inganci a shekarar 2026, wadda ta hada da fadada kashe kudade, da inganta karfin kashe kudi mai zaman kansu na gwamnatocin sassan kasar, da kuma karfafa garanti ga muhimman fannoni.
Taron ya kuma bayyana ayyukan kudi na 2026, wadanda ke da bukatar wadannan muhimman ayyuka: Na farko, a sanya bukatar cikin gida a kan gaba, da kuma goyon bayan gina kasuwar cikin gida mai karfi. Na biyu, a goyi bayan hadin kai mai zurfi tsakanin kirkire-kirkire na fasaha da na masana’antu, da kuma hanzarta bunkasa, da fadada sabbin abubuwan dake haifar da ci gaba. Na uku, a inganta hadewar birane da karkara, da kuma hadin gwiwa tsakanin yankuna don fadada hanyoyin ci gaba. Na hudu, a kara inganta guraben aikin yi, da karuwar kudin shiga ga mazauna birane, da kuma karfafa garantin rayuwar mutane yadda ya kamata. Na biyar, a inganta cikakken sauyi mai kiyaye muhalli ga tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da kuma hanzarta gina kyakkyawar kasar Sin. Na shida, a karfafa musaya da hadin gwiwa kan harkokin kudi da tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, da kuma tallafawa fadada bude kofa ga waje a matsayin koli. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link