’Yan bindiga sun kashe mutum 2 ’yan gida ɗaya a Gombe
[ad_1]
’Yan bindiga sun kashe mutum biyu ’yan gida ɗaya, tare da sace wasu shida a wani hari da suka kai garin Pindiga, da ke Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na daren ranar Asabar, 28 ga watan Disamba, 2025, a kan hanyar Pindiga zuwa Kashere.
A cewar ’yan sanda, maharan sun fara kai hari gidan Mohammed Yusuf, inda suka harbe Yusuf Mohammed mai shekaru 31 da Faiza Mohammed mai shekaru 28.
Dukkaninsu sun rasu a asibiti.
Har ila yau, ’yan bindigar sun sace wata yarinya mai shekaru 16 mai suna Zainab Mohammed Yusuf.
Daga nan sai suka wuce gidan Alhaji Yayaji Abdullahi, inda suka sace matarsa da ’ya’yansa biyu.
Waɗanda aka sace sun hada da Jummai Alhaji Yayaji mai shekaru 35, Al’amin Alhaji Yayaji mai shekaru 11, da Fatima Abdullahi mai shekaru 14.
’Yan sanda sun ce an kai mutanen da aka harba zuwa Asibitin Cottage da ke Pindiga, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da ayyuka, ya jagoranci manyan jami’ai zuwa wajen da abin ya faru.
Bayan isarsu, sun gano harsasai guda shida da aka harba da kuma wani harsashi guɗa ɗaya.
Bayan harin, rundunar ’yan sandan ta ce ta ƙara tsaurara tsaro tare da fara bincike.
Ta ce ta haɗa kai da mafarauta da ƙungiyoyin sa-kai na yankin domin ceto waɗanda aka sace da kuma kama ’yan bindigar.
Rundunar ta yi Allah-wadai da harin, tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za su ɗauki matakan da suka dace domin ganin an kama masu laifin.
Sun kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link