’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata.
A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman Aliyu na garin Zogirma a Ƙaramar Hukumar Bunza.”
Ya ce shanun na daga cikin guda 68 da ake zargin ’yan bindigar Lukurawa sun sace sannan suka tsallaka da su zuwa Nijar a ranar 20 ga watan Agusta.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya jinjina wa DPO na Bachaka da tawagarsa bisa wannan nasara, yana mai kira gare da su ƙara jajircewa wajen kare al’umma.
Kwamishinan ya kuma jaddada cewa rundunar za ta ƙara ƙaimi wajen cafke duk mambobin ƙungiyar tare da ƙwato sauran shanun da aka sace.
Ya roƙi al’ummar jihar da su kasance masu lura da gaggauta bayar da bayanai kan duk wani motsi da ba su aminta da shi ba zuwa jami’an tsaro mafi kusa domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link