Hukumar Hisbah Ta Kano Ta Karɓi Ƙorafe-Ƙorafe Sama Da 12,000 A Shekarar 2025
[ad_1]
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta karɓi jimillar ƙorafe-ƙorafe 12,446 daga al’ummar jihar a cikin ƙananan hukumomi 44, daga watan Janairu zuwa Disambar 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton ayyukan hukumar na shekarar 2025 da Mataimakin Kwamandan Hisbah, Dakta Mujahiddeen Aminuddeen, ya fitar.
- Ganduje Ya Dakatar Da Shirin Kafa Hukumar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano
- Hisbah Ta Kama Mutane 9 Kan Yawon Dare A Kano
Rahoton ya bayyana cewa hukumar ta yi nasarar warware rigingimu 1,908 a cikin shekarar, tare da aiwatar da ayyukan sintiri da tilasta bin doka guda tara a sassa daban-daban na jihar.
Haka kuma, an kama mutane 132 da ake zargi a yayin ayyukan, yayin da mutane 93,231 maza da mata suka amfana ko suka samu ayyukan hukumar a cikin shekarar.
Rahoton ya ƙara da cewa Hisbah ta kula da manyan shari’o’i 4,246 a shekarar 2025, tare da bayyana cewa kuɗaɗen da aka tara daga basussuka, da tarar laifuka da diyya sun kai Naira ₦145,406,409.00.
[ad_2]
Source link