Yadda Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan ‘Yan Jarida 7 A Gombe

[ad_1]

Khalid Idris Doya

Wani mummunar hatsarin sakamakon fashewar tayar mota ya hallaka ‘yan jarida bakwai a kan hanyar Billiri zuwa Kumo da ke jihar Gombe a yayin da suke hanyarsu ta dawowa daga daurin auren abokiyar aikinsu a karamar hukumar Billiri da ke jihar a ranar Litinin.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da ma’aikatan gidajen talabijin mallakin gwamnatin tarayya (NTA) da ke Gombe su 6 da wata ‘yar jarida guda daya lamarin da ya sanya jama’a cikin jimami.

  • Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Neman Belin Malami
  • Buƙatar A Sake Duba Sabuwar Dokar Haraji

Shugaban ‘yan jarida na kasa, (NUJ), Alhassan Yahya, ya bayyana matukar alhinisa kan wannan babban rashin da ‘yan jarida suka yi. Ya ce ranar ta zama ranar bakin ciki ga ‘yan jarida a jihar Gombe.

Ma’aikatan NTA da suka rasa rayukansu a hatsarin sun hada da Manu Haruna Kwami, Manajan sashin mulki; Zarah Umar, Manhajar sashin labaru; Isa Edita a gidan talabijin din; Musa Tabra, tsohon manajan sashin labaru; Aminu, matukin motar da kuma Adams wanda ke kula da sashin Startimes na gidajen talabijin din.

Sai kuma dayan ‘yar jaridan da ita ma ta rasa rayuwarta a wannan hatsarin Misis Judith, wacce ma’aikaciya ce a ma’aikatar yada labarai ta jihar Gombe wacce ta ke aiki a hukumar samar da ilimi a matakin farko na jihar (SUBEB) a matsayin jam’iyar watsa labarai.

Bayan wadanda suka rasa rayukansu, akwai kuma sauran ‘yan jaridan da suka gamu da munanan raunuka da suka hada da Emmanuel Akila wakilin NTA a gidan gwamantin jihar, Nina da Jonathan Bara wadanda a halin yanzu suke kan amsar kulawar likitoci.

LEADERSHIP Hausa ta labaro cewa ko a ranar Juma’ar da ta gabata wasu ‘yan asalin kauyen Lawanti da ke karamar hukumar Akko ta jihar Gombe su bakwai (7) sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure a jihar Borno. Wadanda hatsari a jeren sun jefa jama’an Gombe cikin tsaninin jimami da alhini.

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya samu mummunan labarin hatsarin da ya faru da ‘yan jarida, ma’aikatan Hukumar Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) Gombe, da Ma’aikatan Yada Labarai cikin tsananin bakin ciki, firgici da juyayi.

A sanarwar da Kakakinsa Isma’ila Uba Misilli ya fitar, gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hatsarin a matsayin wani mummunan lamari mai tayar da hankali wanda ya jefa Jihar Gombe cikin jimami, yana mai cewa rashin ya wuce na iyalai da hukumomi, ya ma taba ruhin kafofin watsa labarai da ma’aikata baki daya.

Gwamnan ya ce mamatan kwararru ne da suka sadaukar da rayuwarsu wajen fadakarwa, ilmantarwa da kuma yi wa jama’a hidima, yana mai bayyana mutuwarsu a matsayin mummunan koma-baya ga aikin jarida, da ayyukan gwamnati da kuma shugabanci a Jihar Gombe.

“Wannan ibtila’in abin tausayi ne kwarai. Mun rasa abokan aiki, abokan hulda a fagen ci gaba, kuma ma’aikatan gwamnati masu himma wadanda suka yi aiki tukuru da kuma jajircewa. Za mu dade muna jimamin wannan rashin a tsawon lokaci,” in ji Gwamnan.

Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da shugabanni da membobin kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya, da shugabanni da ma’aikatan hukumar talabijin ta Nijeriya NTA da kuma dukkanin ‘yan jarida da ma’aikatan kafofin watsa labarai a ciki da wajen Jihar Gombe.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *