Malami Zai San Makomar Neman Belinsa Ranar 7 ga Janairu
[ad_1]
Tsohon Atoni Janar na Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da wasu da aka tsare tare, za su ci gaba da zama a Gidan Gyaran Hali na Kuje har zuwa ranar 7 ga Janairu, lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan buƙatar belinsu.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya sanya ranar bayan lauyoyin ɓangarorin biyu sun gabatar da hujjoji masu goyon baya da masu adawa da neman belin. Malami, da ɗansa Abdullaziz, da Asabe Bashir na fuskantar shari’a bisa zargin aikata almundahana.
- Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Neman Belin Malami
- Gwamnati Na Tuhumar Malami Da Ɗansa Kan Laifuka 16 Na Almundahanar Kuɗaɗe
Rahotanni sun nuna cewa kafin fara shari’ar a ranar Juma’a, jami’an Hukumar EFCC da ta Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) sun samu saɓani a Kotun Tarayya da ke Abuja kan batun tsarin tsaro yayin shari’ar tsohon ministan.
An ce rigimar ta taso ne kan wace hukuma ce za ta riƙe alhakin tsaro a yayin zaman kotun. A ranar 30 ga Disamba, kotu ta bayar da umarnin tsare Malami a Kuje har zuwa 2 ga Janairu, domin sauraron buƙatar belinsa.
Rahoton ya ƙara da cewa saɓanin ya kai ga barazana tsakanin jami’an ɓangarorin biyu, inda kowanne ke iƙirarin riƙe ikon tsaro a ƙofar kotun.
[ad_2]
Source link