Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Taurarin Dan Adam Na Sadarwar Intanet
Da misalin karfe 7 da minti 26 na safiyar yau Jumma’a 26 ga watan Disamba ne, a cibiyar harba taurarin dan Adam irin na kasuwanci ta lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, aka yi amfani da rokar Long March-8A, don harba wani rukunin taurarin dan Adam na sadarwar intanet zuwa sararin samaniya cikin nasara, wadanda suka riga suka shiga cikin da’irarsu yadda ya kamata. (Murtala Zhang)