Yadda Takaddama Ta Kaure Bayan Ceto Daliban Neja 130
[ad_1]
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta samu nasarar kubutar da yara ‘yan makaranta 130, wadanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar firamare da sakandire ta St Mary da ke Papiri a Jihar Neja.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Sunday Dare ne ya sanar da hakan a shafinsa na D, ranar Lahadin da ta gabata.
- Rahoton KPMG Ya Shaida Karfin Gwiwar Kamfanonin Kasa Da Kasa Game Da Bunkasar Tattalin Arzikin Sin A 2026
- Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno
“An sake sakin wasu daliban Jihar Neja 130 da aka sace, babu ko daya da aka yi garkuwa da su,” in ji Dare, a cikin sakon da ya wallafa a shafin nasa.
Sai dai, limamin cocin Katolika na Diocese a Kontagora ya dage cewa; daga tasu kididdigar, dalibai da ma’aikata 165 ne suka bace, ba 130 kamar yadda aka bayyana ba.
Har ila yau, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a ranar 21 ga watan Nuwamba, sun kai hari makarantar ta Katolika, inda suka yi awon gaba da dalibai 315 ciki har da ma’aikata. Kazalika, mutane 50 ne suka tsere tun da farko, sannan kuma an sako 100 daga cikinsu daga baya, wanda ya kawo adadin wadanda suka samu suka kubuta su kimanin 150.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, 50 daga cikin daliban; sun samu kubuta bayan sa’o’i 24 da sace su, yayin da aka sako 100 daga cikinsu a ranar 8 ga watan Disamba, inda 165 ke hannunsu.
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP cewa, an sako yaran ne a ranar Asabar, sannan kuma an gan su a cikin wasu motoci kirar bas masu sulke, daga dajin yankin Wawa da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, bisa jagorancin jami’an tsaro.
Majiyar ta ce “Na ga yaran a cikin motocin bas din a cikin wani dogon ayari na motoci masu sulke, jeep da bas, tare da tsaro sosai; kuma sun fito daga dajin Wawa.”
Wata majiya kuma ta bayyana cewa, an sako wasu daga cikin yaran tun da farko, amma ba su kammala zuwa ba, sai da safiyar Lahadi.
Bidiyo da hotuna, sun nuna motocin da aka sako yaran da malamansu.
Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa; ba a sansani daya aka ajiye yaran ba; shi yasa aka sake su daban, bisa tsarin da aka fara tun a daren ranar Alhamis.
Wata majiya ta rawaito cewa, an ga dogayen ayarin motoci dauke da yaran da ma’aikata a kan hanyarsu ta zuwa Minna, babban birnin Jihar Neja, domin mika yaran ga Gwamna Mohammed Umaru Bago a hukumance.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Neja (PPRO), Wasiu Abiodun, ya tabbatar da sakin yaran.
“Wannan zai zama babban Kirsimeti a gare ni, sannan kuma, ina da kyakkyawan fatan cewa; dukkaninsu suna cikin koshin lafiya, amma batu na gaskiya shi ne, na samu kaina a cikin matukar damuwa. Don haka, yanzu muna jiran gwamnati ta kira mu,” in ji shi.
Babban sakataren yada labarai na Gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim ya ce; gwamnatin jihar za ta bayar da dukkannin wasu bayanai ga al’ummar jihar.
Shi ma, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Bayo Onanuga ya ce; daliban darikar Katolika da aka sako sun isa Minna tun a ranar litinin, sannan kuma sun hadu da iyayensu, domin yin bikin Kirsimeti tare.
Onanuga, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na D ya ce; “A yanzu, an sako sauran ‘yan makaranta 130 da ‘yan ta’adda suka sace a makarantar Katolika ta St Mary da ke Papiri a Jihar Neja, a ranar 21 ga watan Nuwamba, inda kuma aka wuce da su zuwa Minna a ranar Litinin da ta gabata, domin yin bikin Kirsimeti tare da iyayensu da sauran ‘yan’uwa.
Yan ta’addan, sun sako dari a baya, wanda ya kawo adadin daliban da aka sako zuwa 230.
“’Yancin yaran, ya biyo bayan wani aikin sirri da sojoji suka yi,” in ji shi.
Daliban Papiri da aka ceto, Abiodun ya jinjina wa Tinubu, ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su ba shi gagarumin goyon baya.
Har ila yau, Gwamnan Jihar Ogun, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu, Prince Dapo Abiodun, ya bayyana farin cikinsa da sako dalibai 130 na makarantar Katolika da aka yi, a garin Papiri da ke Jihar Neja.
Ya kara da cewa, wannan alama ce da ke nuna cewa; miyagun dakaru ba za su yi nasara a kan Nijeriya ba.
A cewar gwamnan, sakin sauran daliban, wanda ya kawo adadin wadanda aka ceto zuwa 230, ya cika alkawuran da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauka na tabbatar da ‘yancinsu, ba tare da wata matsala ba da kuma saukaka haduwa da iyayensu.
Da yake yaba wa shugaban kasar kan matakan tsaro da aka dauka, wanda ya ce; ya dawo da kwarin gwiwar ‘yan Nijeriya a gwamnatinsu, Abiodun ya ce; jerin mutanen da aka yi garkuwa da su da suka hada da 24 daga Jihar Kebbi, 100 daga makarantar Katolika a Jihar Neja, da kuma mabiya addinin Kirista a Eruku, Jihar Kwara, ya nuna cewa; shugaban na da karfin fuskantar kalubalen Nijeriya.
Abiodun, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta ranar Lahadi ya ce; abin farin ciki ne musamman yadda daliban da iyayensu za su yi bikin Kirisimeti cikin farin ciki da rungumar juna, bayan da suka shiga mawuyacin hali.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su tabbatar an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika gwargwadon yadda doka ta tanada.
Ya ce, “Na yi matukar farin ciki da samun labarin cewa; an sako sauran dalibai 130 na makarantar Katolika da ke yankin Papiri a Jihar Neja, wadanda aka yi garkuwa da su.
“Dalibai da iyayensu da sauran al’ummar Papiri da Gwamnatin Jihar Neja, duk sun sha matukar wahala sosai, kuma ina taya su farin ciki a wannan lokaci da aka samu nasara a kan ‘yan ta’addar da su kwashi daliban da ba su ji ba, ba su gani ba tare da malamansu a harabar makarantar.
“Idan har wannan lamarin ya nuna wani abu, tabbas gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata a Nijeriya, sannan kuma ta cancanci addu’o’i tare da goyon bayan kyawawan ayyukanta.
“Shugaban kasa ya kuduri aniyar magance tashe-tashen hankula na garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci tare da dawo da hayyacin al’ummarmu, wanda hakan ba makawa zai dawo da kwarin gwiwar ‘yan Nijeriya da sauran kasashen duniya, kan gwamnati da kuma samar da ci gaba mai tarin yawa.”
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jiya a Abuja, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ya ce; sakin rukunin karshe na mutanen da aka yi garkuwa da su, na nuna wani lokaci na nasara da kuma samun sauki ga al’ummar kasar nan, musamman ga iyalan wadanda abin ya shafa.
“Har ila yau, gwamnatin tarayya za ta tabbatar da ganin cewa, an kubutar da dukkan daliban makarantar Katolika da ke Papiri, wadanda adadinsu ya kai 230, ya kasance babu ko daya daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su,” in ji shi.
A cewarsa, daliban 130 da aka ceto kwanan nan, an mika su ga Gwamnatin Jihar Neja, inda daga bisani kuma, suka sake haduwa da iyayensu.
Ministan ya bayyana wannan farmakin a matsayin wani jajircewa da jami’an tsaron Nijeriya suka yi, inda ya bayyana cewa; ya sake jaddada aniyar kasar na kare ‘yan kasar, musamman kananan yara masu rauni.
“Wannan jajircewa, kokarin da jami’an tsaronmu ke yi ne na tabbatar da aniyar kasarmu ta kare al’ummarta,” in ji Idris.
Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na matukar tausaya wa iyaye da masu kula da daliban, bisa irin halin da suke ciki na sace yaran tare da mika sakon fatan alheri ga iyalan, bayan sun sake haduwa.
“Gwamnatin tarayya ta jajanta wa iyaye da masu kula da yaran a kan radadin da suka samu na sace wadannan yara, tare da yi musu fatan yin bukukuwan Kirsimeti lafiya,” in ji sanarwar.
Aikin ceton, ya kawo rufe wani babi mai radadi ga al’ummar da abin ya shafa, yayin da hukumomi ke jaddada aniyarsu na inganta tsaro da kuma kiyaye makarantu a fadin kasar baki-daya.
[ad_2]
Source link