Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya

[ad_1]



Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro.

’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji.

Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe.

Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba.

Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram suka addaba shekaru da dama.

A wasu yankuna, an buɗe makarantu a sansanonin ’yan gudun hijira domin yara su samu damar ci gaba da karatu, amma a yawancin ƙauyuka makarantu sun daina aiki gaba ɗaya, lamarin da ya tilasta dubban yara daina zuwa makaranta.

Ga yadda jadawalin ya kama a jihohi:

  • Zamfara: An rufe makarantu 20 na firamare da 19 na sakandare, wasu kuma sojoji ne amfani da su.
  • Neja: Makarantu 18 na firamare, guda ɗaya ta sakandare da 11 na Fulani duk an rufe su, da dama sun koma sansanin sojoji.
  • Sakkwato: An rufe Makarantu shida, wasu ’yan gudun hijira ko ’yan bindiga ke amfani da su.
  • Katsina: An rufe makarantu 52 bayan yawaitar hare-hare da satar ɗalibai.
  • Kaduna: Aƙalla makarantu shida suka daina aiki sakamakon mazauna ƙauyukan sun yi hijira.
  • Kebbi: An rufe makarantu bayan satar ɗalibai 96 a Birnin Yauri a 2021.
  • Benuwe: An rufe makarantu 55 a 2024, yanzu ’yan gudun hijira ne ke zaune a cikinsu.
  • Kwara: An rufe wasu makarantu a Ƙaramar Hukumar Patigi bayan yawaitar hare-hare ’yan bindiga.

Matsalar da ilimi ke fuskanta

Najeriya tana daga cikin ƙasashen da suka fi yawan yara da ba sa zuwa makaranta ba.

UNICEF ta ƙiyasta cewa yara miliyan 10.2 masu shekarun zuwa firamare da miliyan 8.1 masu shekarun zuwa sakandare ne ke zaune a gida ba tare da makaranta ba.

Katsina, Kebbi da Sakkwato sun kowa yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta, inda kowace jiha ke da aƙalla yara miliyan ɗaya.

Masana sun ce wannan matsala na haifar da mummunan makoma ga Najeriya.

UNICEF ta yi gargaɗin cewa kowace a duk shekara idan aka samu yaron da baya zuwa makaranta, hakan na ƙara jefa shi cikin hatsarin faɗawa cikin talauci.

Masana tsaro kuma sun ce idan ba a ɗauki mataki ba, samari da ba sa zuwa makaranta na iya shiga ayyukan ta’addanci da aikata munanan laifuka, yayin da ’yan mata za a tilasta musu yin aure da wuri, ko kuma shiga karuwanci da sayar da kaya a titi.

Sun jaddada cewa idan ba a magance wannan matsala ba, ƙasar za ta fuskanci ƙarin jahilai, talauci da tashin hankali.

Iyaye da shugabannin al’umma suna roƙon gwamnati da ta magance matsalar tsaro domin yara su samu damar komawa makarantu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *