Yara 4 da wasu mutum 8 sun rasu a hatsarin mota a Imo
[ad_1]
Aƙalla mutum 12; ciki har da yara huɗu ne suka rasu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Owerri zuwa Onitsha da ke Jihar Imo.
Hatsarin ya auku ne lokacin da wata tankar gas mai lamba T 16716 LA, mai ɗauke da rubutun NUPENG, ta ƙwace daga kan hannunta ta afka wa wata motar fasinja.
Motar na ɗauke da mambobin Ikklisin Jehovah’s Witness daga Jihar Anambra zuwa ƙauyen Agwa da ke Jihar Imo.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da mutuwar manyan mutane takwas da wasu yara huɗu, yayin da wasu takwas suka jikkata.
An kai mamatan a ɗakin ajiyar gawarwaki na Ogbaku Mortuary, yayin da aka kwantar da waɗanda suka jikkata a Asibitin Divine Hospital Awo-Omamma.
Okoye, ya ce an fara bincike gano musababbin aukuwar hatsarin.
Ya ce tuni aka buɗe hanyar, yayin da jama’a suka ci gaba da zirga-zirga.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link