Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa
[ad_1]
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulƙadir Muhammad, ya tabbatar da naɗin Burgediya Janar Marcus Kokko Yake (mai ritaya) a matsayin sabon Sarkin Ƙabilar Sayawa (Gung Zaar), a matakin Sarki mai daraja ta ɗaya.
A lokacin da yake karɓar takardar tabbatar da naɗin nasa a ranar Litinin, sabon Gung Zaar ya yi alƙawarin shugabanci mai cike da adalci, gaskiya da riƙon amana, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummar Sayawa.
Janar Yake ya nuna godiyarsa ga Gwamna Bala Muhammad bisa wannan gagarumar amincewa da ya yi masa, tare da ba da tabbacin yin aiki tukuru don ganin Sayawa da Jihar Bauchi sun ci gaba da samun nasara a fannoni daban-daban.
Ya roƙi haɗin kai daga sauran sarakuna, shugabanni da jama’a domin tafiya tare wajen wanzar da cigaba da zaman lafiya. A cewarsa, nasarar kowane Sarki tana dogara ne da goyon bayan mutanensa da haɗin kai tsakanin al’umma.

Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung Zaar.
[ad_2]
Source link