Matan Habasha Sun Samu Horo Karkashin Tallafin Bunkasa Kasuwanci Na Sin

[ad_1]

Shirin kasa da kasa na horar da mata sana’o’i ko GFEEP, wanda gwamnatin kasar Sin ke tallafawa, ya horar da mata mamallaka sana’o’i su 60 a kasar Habasha.

An gudanar da horon samun kwarewar gudanar da sana’o’in na mako biyu ne a birnin Addis Ababa fadar mulkin Habasha, ya kuma kunshi ajujuwan kaifafa basirar kasuwanci, da ilimin dijital, da sabbin dabarun aiwatar da kasuwanci, da kwarewa a fannin gudanar da sana’o’i.

Da yake tsokaci yayin bikin kammala horon a ranar Asabar, mukaddashin jakadan Sin a Habasha Sun Mingxi, ya ce shirin samar da horon muhimmin ginshiki ne na gina kwarewar kasuwanci, karkashin shirin aiki na dandalin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka na birnin Beijing, wanda aka tsara gudanarwa tsakanin shekarar nan ta 2025 zuwa 2027, da nufin karfafa gwiwar mata da ingiza daidaiton jinsi a kasashen nahiyar Afirka.

A nasa jawabin kuwa, mataimakin babban sakataren hukumar bunkasa cinikayya ta kasar Habasha Tsedeke Digafe, cewa ya yi horon ya zamo kyakkyawan misali, na yadda Habasha da Sin ke kara azamar bunkasa daidaiton jinsi da cimma nasarar ajanda ta biyar, cikin kudurorin samar da ci gaba mai dorewa na MDD. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *