Yakin Iran: Duniya Na Fuskantar Tsadar Kayan Abinci Da Man Fetur
[ad_1]
Rikicin da ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya, ya fara shafar Nijeriya kai tsaye, sakamakon tashin farashin danyen mai a duniya, lamarin da ya haifar da karin farashin sufuri da kuma farashin kayan abinci a sassa da dama na kasar.
A manyan biranen kasar da suka hada da Legas, Abuja, Kano, Kaduna, Fatakwal da Yenagoa, masu ababen hawa na kokawa da sabon farashin man fetur, wanda a halin yanzu ya kai daga tsakanin naira 1,020 zuwa N1,100 kan kowace lita a gidajen sayar da man da dama.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe
- Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara
Wannan matsala ta haifar da damuwa a tsakanin mazauna wadannan yankuna, musamman ga masu harkar sufuri da kuma ’yan kasuwa, wadanda ke fargabar karuwar za ta iya sake kawo tabarbarewar tsadar rayuwa da kuma sauran al’amuran yau da kullum.
Sabon tashin farashin man fetur din na da nasaba da tashin farashin danyen mai a duniya, biyo bayan tashin hankalin da ya barke a tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, lamarin da ya kawo cikas ga hasashen samar da man a kasuwannin mai na kasa da kasa.
An samu hauhawar farashin man a Legas, Abuja, Kano, Fatakwal da sauransu.
A Legas, matafiya da magidanta sun ce; tuni sun fara kashe kudade wajen sufuri da sayen kayan abinci, biyo bayan karin farashin man fetur din da aka samu.
Binciken da Daily trust ta yi a gidajen mai da dama ya nuna cewa; yanzu ana sayar da kowace litar mai a tsakanin naira 1,050 zuwa naira 1,100, ya danganta da gidan man.
A gidajen sayar da man fetur na Northwest Petroleum, ana sayar da man a kan kusan naira 1,050 kan kowace lita, yayin da gida mai na TotalEnergies, ke sayar da shi a kan naira 1,055 kan kowace lita.
Kamfanonin mai na MRS, suna sayar da shi a kan kusan naira 1,057, yayin da Kamfanonin Mobil ke karbar naira 1,100 kan kowace lita.
Tashin farashin man fetur din, ko kadan bai haifar da da mai ido a sassan sufuri da na abinci ba, lamarin da ya kara sanya kashe kudade a hidimomin yau da na kullum, musamman ga matafiya da kuma magidanta, wadanda tuni suka fara kokawa da wannan tsada ta rayuwa.
Masu safarar kayayyaki na kasuwanci, sun fara daidaita farashin kayayyakinsu da farashin man fetur, saboda tsadar da man din ya yi.
Ekundayo Oladimeji, wani direban haya na bas da ke zirga-zirga tsakanin Ogba da Ikeja, ya tabbatar da cewa; tuni farashin sufuri ya tashi daga naira 400 zuwa naira 500, sakamakon tashin farashin man fetur.
“Babu shakka, akwai yiwuwar kara kudin sufuri, mun fara karbar naira 500 daga Ogba zuwa Ikeja.
“A ranar Litinin, zai iya karuwa zuwa naira 700. Na sayi mai a kan N935 a ranar Juma’a, amma a safiyar jiya (Asabar) na sayo shi kan N1,057, kuma farashin na iya ci gaba da karuwa,” in ji shi.
Wasu masu jigilar kayayyaki sun ce, suna kokawa saboda juriyar da fasinjoji suke da ita, musamman idan aka lura da yadda farashin yake yanzu.
Nelson, wanda ke kula da titin Ogba–Agege, ya ce; “Ba mu kara farashin ba, saboda tuni fasinjoji dama suna kokawa a kan farashin kudin da ake biya a halin yanzu, amma karin farashin man fetur ya shafi kudaden da muke kashewa, sannan ya kuma rage ribar da muke samu.”
Har ila yau, ana kuma ganin tasirin karin farashin man fetur a kasuwannin abinci da ke fadin Jihar Legas, inda farashin jigilar kayan amfanin gona ya yi tashin gwauron zabi.
‘Yan kasuwan dai sun ce, farashin barkono da tumatur, sun yi tashin gwauron zabo a cikin kankanin lokaci, inda suka ce; farashin sufuri ya yi matukar tsada.
Yanzu haka, ana sayar da barkono a kan naira 82,000, idan aka kwatanta da naira 18,000 a baya.
Matsakaicin buhu ya karu zuwa kusan naira 122,000 daga naira 22,000, yayin da babban buhu ya kai kusan naira 172,000, idan aka kwatanta shi da kusan naira 70,000 a baya.
Haka zalika, farashin tumatur ya yi tashin gwauron zabi, inda a baya ake sayar da buhu kan naira 22,000, yanzu kuma ya kai kimanin naira 50,000, yayin da babban buhu ya tashi daga kimanin naira 62,000 zuwa naira 125,000.
Oyekale Oluwasegun, wani mazaunin Legas da ke yin zirga-zirga a kullum don zuwa aiki, ya ce; karin kudin da aka yi masa ya shafi kudaden da yake kashewa duk wata.
A cewarsa, tafiya daga Powerline zuwa Ogba, wanda a baya yake biyan naira 200, yanzu ya kai naira 300.
“Na riga na kasafta kudina da zan kashe a wata, amma wannan karin ya rusa min lissafin nawa,” in ji shi.
“Na fahimci cewa, tattalin arziki yana fuskantar matsin lamba daga wasu dalilai na waje, amma akwai bukatar gwamnati ta dauki matakin gaggawa kafin lamarin ya kara tabarbarewa.”
Wasu gidajen man a Legas da Abuja da Kano a ‘yan kwanakin da suka gabata, wadanda suka hada da AY Maikifi, Aliko Oil da AA Rano, sun daidaita farashin famfunansu daga kimanin naira 980 kan kowace lita zuwa tsakanin naira 1,050 zuwa naira 1,104, yayin da wasu gidajen man suke sayarwa a kan naira 1,060, kan kowace lita.
A gidajen man da ke karkashin Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC), ana sayar da man fetur a kan Naira 1,084 kan kowace lita, yayin da AMMASCO da ke titin Kotu ke sayar da man a kan naira 1,104 a ranar Lahadi.
Wani mazaunin garin, Abubakar Danzaria, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro, inda ya yi gargadin cewa; karin farashin man da ake yi a lokuta daban-daban na iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasar, idan har aka ci gaba da hakan.
“Muna gudanar da azumin watan Ramadan, kuma babu zato babu tsammani farashin mai yana karuwa akai-akai,” in ji shi.
Masu harkar sufuri a jihar, sun kara kudin sufuri a jihar, sakamakon tashin farashin man fetur.
Saifullahi Rabi’u, mai sana’ar tuka Adaidaita Sahu a Kano, ya ce; ya sayi man fetur a kan naira 1,060, kan kowace lita a gidan mai a karshen makon da ya gabata.
“Lokacin da farashin mai ya karu, dole ne mu daidaita namu farashin,” in ji shi. “Idan muka ci gaba da cajin adadin abin da muke caza a da, ko shakka babu za mu yi asara,” in ji shi.
A wasu sassan Abuja, yanzu ana sayar da man fetur a tsakanin naira 1,050 zuwa 1,080, ya danganta da wurin da ake sayar da mai, sabanin yadda yake a da a tsakanin N845 zuwa N875.
[ad_2]
Source link