Kasar Saudiyya Ta Kaddamar Da Shirin Yi Wa Yara Aikin Tiyatar Kunne A Abuja
[ad_1]
Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman ta Saudi Arabiya (KSRelief), ta Kaddamar da wani shiri na musamman na dasa na’urar kara ji, ga masu matsalar kunne a Abuja, wanda ke nuna wani babban agajin jin kai da nufin magance matsalar rashin ji a tsakanin yara kanana a Nijeriya.
Shirin na aiwatuwa ne tare da hadin gwiwar hukumomin kiwon lafiya na Nijeriya, wanda ake sa ran yi wa akalla yara 30 wannan tiyata, da nufin maido da jinsu tare kuma da ba su da damar shiga cikin al’umma.
Shirin na samun cikakkiyar kulawa, ta hanyar yin gwaje-gwaje, tiyata, bibiya, jinya na ji da kuma gyaran magana.
Mai girma jakadan ofishin jakadancin kasar Saudiyya a Nijeriya, Saad bin Fahd Al-Marri, ya yaba wa wannan hadin gwiwa tare da jaddada muhimmancin jin kai da aikin ke da shi.
“Wannan shirin yana nuna sadaukarwar masarautar, domin tallafa wa al’ummomi masu rauni da kuma karfafa tsarin kiwon lafiya a kasashen da ke abokantaka da ita. Ta hanyar KSRelief, mun himmatu wajen samar da mafita ta gaske, wadda zai dawo mana da burin da muke da shi, ta canza rayuwarmu da kuma zurfafa dangantakar da ke tsakanin Saudi Arabiya da Nijeriya,” in ji shi.
Shirin dasa wannan na’ura ta kara ji, ta ginu ne kan ci gaba da kasancewar Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman ta Saudi Arabiya (KSRelief), na jin kai a Nijeriya da kuma fadin nahiyar Afirka baki-daya, inda cibiyar ke tallafa wa ayyukan jinya, shirye-shiryen magance cututtuka da kuma ayyukan agaji ga al’ummomin da ke fama da rikici ya shafa.
Hakan na kara jaddada aniyar masarautar Saudiyya, a karkashin jagorancin mai kula da masallatan Harami guda biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz da kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, na ciyar da muhimman tsare-tsaren kiwon lafiya da bayar da tallafi na jin kai ga al’ummar da ke neman taimako da agaji a duniya.
[ad_2]
Source link