NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi A Najeriya
[ad_1]
Ƙarin Podcasts
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha nanata muhimmancin samar da ’yan sandan jihohi a Najeriya, yana mai cewa hakan na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar.
Shugaban ya bayyana cewa tsarin ’yan sanda da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya kaɗai ba zai iya biyan buƙatun tsaro na ƙasa mai yawan jama’a da faɗi kamar Najeriya ba.
A wani mataki na ci gaba da duba yiwuwar aiwatar da wannan tsari, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, jim kaɗan bayan kama aikinsa ne ya kafa wani kwamiti na musamman domin nazartar hanyoyin da za a bi wajen samar da ’yan sandan jihohi.
Sai dai duk da yadda wasu ke ganin cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro, masana da masu ruwa da tsaki na cewa akwai ƙalubale da dama da ka iya tasowa.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ƙalubalen da shirin samar da ‘yan sandan jihohi zai iya fuskanta.
Domin sauke shirin, latsa nan
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link