’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina

[ad_1]



Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina.

An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina.

Rahotanni sun ce an kai harin ne wajen misalin ƙarfe 3:00 na daren Litinin inda maharan suka sace magidancin mai suna Malam Anas tare da matarsa mai suna Halimatu ​​da ’yarsa.

Bayanai sun kuma nuna wani dan bangar da yayi ƙoƙarin kai musu ɗauki ya rasa ransa.

Sai dai wasu mazauna unguwar sun ce tun da farko sun yi zargin wasu mutane biyu da aka ga suna zirga-zirga a yankin har suka sanar da ’yan bangar da ke unguwar.

Sai dai ko da aka neme su ba a gan su ba, sun buya tun da suka lura jama suna zargin su.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da Kakakinta, DSP Abubakar Sadiq ya fitar.

Ya ce wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun ƙaddamar da harin a ranar Talata a gidan wani Anas Ahmadu, mai shekaru 33, a unguwar Filin Kanada a cikin garin Katsina, inda suka yi garkuwa da shi.

Kakakin ya kuma ce maharan sun yi awon gaba da matar mutumin mai suna Halimatu da ’yarsa Jidda Anas.

Ya tabbatar da cewa, ’yan bindigar sun kuma harbe wani mai suna Abdullahi Muhammad, mai shekaru 25, wanda ke aikin banga, kuma sun tsere daga wurin kafin isowar jami’an ’yan sanda.

DSP Abubakar ya kuma ce rundunar ta shiga yin bincike don gano maharan da kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su.

Mazauna birnin Katsina dai sun fara nuna damuwarsu kan yadda ’yan bindiga ke karuwa a Jihar wanda ta kai har suna shiga cikin manyan biranen jihar suna kai hare-hare.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *