Sojoji Sun Ceto Mutane Takwas Da Aka Sace A Yayin Wani Bikin Aure A Shanono
[ad_1]
Dakarun rundunar Brigedeya 3 ta Sojojin Nijeriya sun ceto mutane takwas cikin goma da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka sace a wurin bikin aure a Dabawa, ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano.
Wata majiya daga shalƙwatar soji ta shaida cewa maharan, waɗanda aka ce sun sanya kayan sojoji, sun kai hari tare da yin awon gaba da mutanen. Dakarun da ke sintiri a bakin Kogin Yankwada sun hanzarta kai ɗauki bayan samun rahoton lamarin, inda suka yi artabu da maharan a ƙauyen Garu da ke maƙwabciyar Jihar Katsina.
- Tinubu, Shettima Zasu Ziyarci Kano Halartar Tarɓar Gwamna Yusuf Zuwa APC
- Rundunar Tsaro Ta Kano Ta Kama Haramtattun Magunguna Na Naira Biliyan 1.5
An ce sojojin sun bi sawun maharan har zuwa kan titin Katsina–Gidan Mutum Ɗaya kafin aka rasa inda sukaa yi. A yayin farmakin, an samu nasarar ceto ’yan mata takwas daga cikin waɗanda aka sace, kuma tuni aka miƙa su ga iyalansu.
Majiyar ta ƙara da cewa ana ci gaba da sintiri a yankin domin gano sauran mutane biyun da har yanzu ba a ceto su ba, tare da ɗaukar matakan hana sake faruwar irin wannan hari.
[ad_2]
Source link