Taron Cika Shekaru 55 Na “Diflomasiyyar Ping-Pong” Ta Sin Da Amurka Ya Gudana A Amurka

[ad_1]

A ranar 3 ga watan Fabrairu bisa agogon Amurka, an gudanar da taron cudanyar al’adu domin cika shekaru 55 na “Diflomasiyyar Ping-Pong” tsakanin Sin da Amurka a makarantar sakandare ta Lincoln da ke Tacoma, a jihar Washington. Wannan taro ya kasance na hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kungiyar jama’ar Sin ta abota da kasashen waje, da kuma kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin.

Babban daraktan CMG, Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta bidiyo inda ya bayyana cewa abota tsakanin kasashe tana ta’allaka ce da fahimtar juna tsakanin al’umma, kuma fahimtar juna tsakanin al’umma tana ta’allaka da sadarwar zukata. A yau, bisa karramawa sosai mun gayyato daya daga cikin ’yan wasan kwallon tebur na Amurka da ta ziyarci Sin a shekarar 1971, domin ta bayyana labarinta daga shekaru 55 da suka gabata.

Ya kara da cewa, mu hadu baki daya wajen sanin darajar “Diflomasiyyar Ping-Pong” da kyakkyawan fata na Sinawa da Amurka da ke aiki tare. Mu ci gaba da rubuta kyawawan labarai na cudanyar al’umma a tsakanin kasashen biyu a wannan sabon zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *