Na yi nadamar alaƙata da Epstein — Bill Gates
[ad_1]
Fitaccen hamshaƙin mai kuɗin nan, Bill Gates ya ce ya yi matuƙar nadamar alaƙar da ya yi tare da Jeffrey Epstein, wanda aka samu da laifukan aikata lalata da ƙananan yara.
Mamallakin kamfanin Microsoft, ya bayyana haka ne bayan fitar da bayanai daga Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, waɗanda suka nuna saƙonnin imel suka nuna yadda manyan mutane suke da alaƙa da Epstein.
A cikin wani saƙon imel, Epstein ya yi iƙirarin cewa Gates ya yi lalata da mata duk da ksancewar yana da aure, kuma yana taimaka masa a ɓoye wajen aikata wasu laifukan, amma Gates ya musanta zarge-zargen gaba ɗaya.
“Na yi nadamar kowane lokaci da na ɓata tare da shi, kuma ina neman afuwa,” in ji Gates a wata hira da ta yi da kafar 9News Australia.
Ya ƙara da cewa saƙon imel ɗin da ya yi wannan iƙirarin ba a aika shi ba don haka ba gaskiya ba ne.
“Ban san dalilin da ya sa ya rubuta hakan ba. Wataƙila yana ƙoƙarin ɓata min suna ne,” in ji shi.
Wani mai magana da yawun Gates ma ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa bayanan kawai sun nuna cewa Epstein ya fusata ne saboda bai samu damar ci gaba da hulɗa da Gates ba, don haka ya yi ƙoƙarin ɓata masa suna.
Tsohuwar matar Gates, Melinda French Gates, ta ce bayanan da aka fitar sun sake tuni mata da wasu al’amura da suka faru a baya marasa daɗi tsakaninta da attajirin.
Ta ce har yanzu akwai ayoyim tambayoyi da ake neman amsarsu game da dangantakar Gates da Epstein.
Ta ce akwai buƙatar mutanen da abin ya shafa, ciki har da tsohon mijinta, su amsa waɗannan tambayoyi.
Bill da Melinda Gates sun rabu da juna a shekarar 2021.
Gates, ya ce ya haɗu da Epstein ne a shekarar 2011, kuma sun gana tare da cin abinci sau uku kacal.
Ya ce bai taɓa ziyartar tsibirin Epstein ba, kuma ba shi da wata alaƙa ta shafi yin lalata da ƙananan yara ba.
Epstein dai ya mutu a gidan yari a 2019 yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi lalata da ƙananan yara.
Rahoton ya kuma nuna cewa samun sunan mutum a cikin takardun Epstein ba hakan na nufin ya aikata laifin da aka zarge shi ba.
Amma takardun sun bayyana alaƙa tsakanin Epstein da mutane da dama da suka taɓa musanta ko daina alaƙa da shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link