Yau Najeriya za ta kece raini da Maroko a gasar cin kofin nahiyar Afirka
[ad_1]
Yau Laraba tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, za ta fafata da Atlas Lions ta Maroko a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) a yau Laraba.
Za a buga wasan ne a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke birnin Rabat, ƙasar Maroko, da ƙarfe 9:00 na dare..
Dukkanin ƙungiyoyin biyu ba su yi rashin nasara ba ko da sau daya tun da aka fara gasar AFCON ta bana.
Najeriya ta lashe dukkan wasanni biyar da ta buga zuwa yanzu, yayin da Morocco ta samu nasara huɗu tare da canjaras a ɗaya.
Wannan shi ne karo na biyu da za su yi arangama cikin shekaru 22 da suka gabata, kuma karo na biyu da za su kece raini a zagayen daf da ƙarshe a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Afirka.
A baya, sun haɗu a wasan daf da ƙarshe na AFCON a shekarar 1980, inda Najeriya ta samu nasara da ci 1-0.
Felix Owolabi ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Super Eagles damar ɗaukar kofin a karon farko a tarihin gasar, wadda aka shirya a birnin Legas.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link