Rikicin PDP: Kotun Koli Ce Kadai Za Ta Warware Lamarin Ba INEC Ba –Bangaren Turaki
[ad_1]
Wani bangare na PDP karkashin jagorancin Kabiru Turaki ya bayyana cewa Kotun Koli ta Nijeriya ce kadai ke da ikon yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa INEC ba ita ce ke da ikon hukuncin karshe ba.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na bangaren, Ini Ememobong, ya fitar, ya ce sun riga sun garzaya zuwa Kotun Koli domin neman hukunci na karshe kan rikicin shugabanci a jam’iyyar.
- Shin Bunkasar Sabbin Fasahohi Na Iya Illata Walwalar Jama’a?
- ADC Ta Nemi Shugaban INEC Ya Yi Murabus
Wannan martani ya biyo bayan matakin da INEC ta dauka na amincewa da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da ke da alaka da Nyesom Wike, inda ta sanya sunayensu a shafinta na hukuma, tare da bayyana Abdulrahman Mohammed a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
An ce Mohammed da sauran mambobin NWC sun fito ne daga wani babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Moshood Abiola National Stadium a Abuja.
Sai dai bangaren Turaki ya ki amincewa da taron, yana mai cewa ba sahihi ba ne, tare da zargin cewa an gudanar da shi ne duk da shari’o’in da ke gaban kotu.
[ad_2]
Source link