’Yan bindiga sun sace mutane 9 a Sakkwato

[ad_1]



An yi garkuwa da mutane tara tare da jikkata wasu biyu a wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar yankin Chacho da ke Ƙaramar Hukumar Wurno ta Jihar Sakkwato.

Wani daga cikin ’yan uwa na waɗanda aka sace, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa maharan da suka zo da yawa sun kutsa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Laraba.

Ya ce sun shigo ta wata hanya da ke haɗe da dajin Sabon Birni, wanda aka daɗe ana alaƙanta shi da mafakar ’yan bindiga.

“Lokacin da aka kawo rahoton harin, da dama daga cikinmu muna kwance a ƙofar gida. Da aka yi ihu cewa ’yan bindiga sun shigo, sai muka tashi muka ranta a na kare. Daga wani ɓangare na kauyen muka ji ƙarar harbe-harbe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa maharan sun yi awon gaba da mata bakwai da dattijai biyu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka kuma yanzu haka suna jinya.

Mutanen ƙauyen sun koka kan yadda hare-haren ’yan bindiga ke ƙara yawaita, suna danganta hakan da rashin jami’an tsaro a yankin.

“Ko da yake ƙauyenmu na da yawan jama’a, babu jami’an tsaro kamar ’yan sanda ko sojoji,” in ji wani mazaunin ƙauyen.

Sun roki Gwamnatin Jihar Sakkwato da ta turo jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba su da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka sace a halin yanzu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *