Ƴar Nijeriya Ta Rasa Lasisin Aiki A Birtaniya Bayan Gano Ta Yi Amfani Da AI A “Interview”
[ad_1]
Wata ƙwararriyar likitan abinci ‘yar Nijeriya ta rasa lasisi a Birtaniya bayan an kama ta da yin amfani da fasahar AI a interview. Lamarin ya faru ne yayin wata hira ta aiki da NHS ta yanar gizo.
Rahotanni sun ce ta riƙa amfani da amsoshin ChatGPT a lokacin tattaunawar neman aiki. Ana zargin ta na neman a maimaita tambayoyi domin samun lokaci kafin bayar da amsa.
- Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI
- Yadda Jigo A APC Na Kano Ya Rasu A Otal A Abuja
Kwamitin masu hira ya fara zargin magudi bayan lura da kamanceceniya da amsoshin AI. Daya daga cikinsu ya gwada saka tambayoyin a ChatGPT inda amsoshin suka yi kama da nata.
An miƙa batun zuwa Hukumar HCPTS wadda ta binciki lamarin. Daga bisani ta yanke hukuncin cewa abin ya saɓawa ƙa’ida tare da cire ta daga rajistar ma’aikata.
Shari’ar ta nuna cewa an yi interview ɗin ne a watan Maris 2024 a asibitin Royal Surrey. An ce ta nuna ƙwarewa a tambayoyin gaba ɗaya amma ta kasa daidaita a batutuwan lafiya.
[ad_2]
Source link