’Yan bindiga sun sace uwa da ’ya’yanta a Kogi

[ad_1]



’Yan bindiga sun sace wata matar aure da ’ya’yanta biyu a yankin Bareke-Egbe a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma da ke Jihar Kogi.

’Yan bindigar sun kai farmaki gidan wani manomi mai suna Tokpe Gody da misalin karfe 2 na dare ranar Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su sace matarsa da ’ya’yansa biyu.

Rahotanni sun ce Gody ya sha da ƙyar amma ya samu raunukan harbin bindiga a jiki da ƙafafuwansa, kuma yana karɓar magani a asibitin Egbe, inda likitoci ke cewa yana cikin mummunan yanayi.

Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Adeyemi ya ce: “Tokpe Gody manomi ne mai fama da yadda zai ciyar da iyalinsa. Ya tsira da ƙyar daga ’yan bindigar, amma matarsa da ’ya’yansa biyu ba su yi sa’a ba, domin sun tafi da su.”

Mazauna yankin sun ce wannan harin ya zo ne kwana guda bayan da aka kashe wani mai babur a garin Ejiba — kusa da Isanlu — bayan da ya afka cikin kwanton bauna da ’yan bindiga suka yi.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kogi ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *